Majalisar Dinkin Duniya ta jadadda cewa albarktun ruwa da ke kwance a karkashin kasa, wanda dan Adam zai iya shan cikin koshin lafiya, na da matukar yawan da zai ishi al’ummar duniya matukar an bi hanyoyin da suka dace.
Asusun Bunkasa Ilimi, Kimiyya da Raya Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ne, ya yi wannan kalami, a wani bangare na bikin Ranar Ruwa ta Duniya da ake gudanarwa duk ranar 22 ga watan Maris na kowace shekara.
Cikin wani rahoto da UNESCO ya fitar, ya ce kaso 99 na dukannin narkakken abu da ke karkashin kasa, ruwa ne, duk da cewa akwai karancin wannan ilimi a tsakanin al’ummar duniya.
Rahoton ya nuna cewa nan da shekara 30 masu zuwa bukatar tsaftataccen ruwa zai karu, la’akari da karuwar jama’a da kuma masana’antu da habbakar ayyukan gona, wadanda dukannin bangarori ne masu bukatar ruwa.
Sai dai daraktan UNESCO, Audrey Azoulay, ya ce sauyin yanayi da gurbacewar muhalli, na busar da ruwan da ke doron duniya, don haka akwai bukatar a gaggauta mayar da hankali wajen amfanar wanda ke boye karkashin kasa.
Kazalika, Azoulay ya ce babbar matsalar a yanzu ita ce hukumomi ba su fara ankara da matsalar ba, wadda kuma za ta yi wa duniya muni idan ba a fara tunkarar ta tun yanzu ba.
Mutane da dama a duniya musamman wasu wurare a yankin Afirka na fama da rashin wadattacen ruwan sha da kuma amfanin yau da kullum.