Hakika ranar Talatar da gabata take ranar ruwa ta duniya, inda hakan yake kara ba ni kwarin gwiwa dangane da tunawa da wannan rana da kuma tunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya, wato marigayi Malam Umar Musa Yar’adua. Domin kuwa tun a lokacin mulkinsa ya wadatar da Jihar Katsina da albarkar ruwa, wanda har ya zuwa yanzu jihar take samun wadataccen ruwan sha. hakika mu dai a Jihar Katsina muna samun ruwa wadatacce kuma tsaftatacce, da haka ne nike so Aminiya ku ba ni wata dama domin inyima shi Wannan bawan Allah wato Malam Umar Musa Yar’adua addu’ar shiga gidan aljanna. Domin hakika ya taka rawar gani a wannan fanni na inganta harkar ruwan sha a lokacin rayuwar sa.
Daga Comrade Sanin Shaga kofar kaura Katsina Jami’in Hulda da jama’a na kungiyar Muryar talaka reshen jihar Katsina 08039433111 [email protected].
Dimokuradiyya ta zauna a Afirka
Assalamu alaikum, Hakika a zabukan da suka gudana a Nijar da Benin wani karin nuna yadda dimokuradiyya ke samun gindin zama a nahiyarmu ta Afirka ne, ganin yadda suka gudana cikin nasara da kuma kwatanta adalci.
Daga Hafizu Balarabe Gusau 07035304499 [email protected]
A kara hakuri da gwamnatin Buhari
Salam. Edita abun naku ko akwai son kai ne? Ni ma’abocin karanta Aminiya ne kowane mako. Sau da yawa ina aiko da sakon ra’ayina ba ku rubutawa na fara dai a filin musha dariya, na sha aikowa ba ku rubuta wa. Sannan a filin sakon waya na sha turowa, shi ma ban gani ba. Ina so ku ba ni fili don in yaba wa gwanina, saboda yabon gwani ya zama dole. Sannan kuma ina kara jan hankalin ’yan uwana talawa ’yan Najeriya su kara hakuri da wannan gwamnati mai albaka. Duk wannan tafiye-tafiyen da Baba Buhari yake yi kasashen waje to babban alkairi ne ga ’yan kasa baki daya. Domin wannan gwamnati ta yanzu ba gwamnatin PDP ba ce, saboda gwamnatin PDP azzalumar gwamnati ce, da cin amanar kasa.
Daga Lawal Isa Mpape, Abuja.
Shawara ga Gwamnatin Buhari
Assalam jaridar Aminiya mai Albarka. Ku mika min shawarata ga Gwamnatin Muhammadu Buhari da damina ta soma nuna alama za ta taimaka wa manoma da duk wani kayan aiki na noma da takin zamani..Mu kuma manoma mu yi kokarin gyara gonakinmu,da samun malaman gona na kusa da mu suna ba mu shawarwari don bunkasa harkan noma a Najeriya.
Daga Hussaini Almusaya Gombe 08130446601.
Ruwan leda ya gagari talaka
Talakan Najeriya tunda ruwan leda ma (pure water) an kara masa kudi mu gode wa Allah, tun da iskar da muke shaka ba ta gwamnati ko ’yan kasuwa ba ce, balle su kara mata farashi.
Daga A.U. Shuwaki karamar Hukumar kunchi, Jihar Kano a Najeriya.
Addu’a ga shugabanni
Salam. Gaisuwa da fatan alkairi ga dukkan ma’aikatan jaridar Aminiya bayan haka ina mika sakon jinjina ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa manufofin wannan gwannatin na alkairi da fatan Allah ya bai wa shugabanninmu damar cika alkawuran d asuka daukar mana amin summa amin.
Daga Ibrahim khaleel jama’are. 08059465281.
Jinjina ga Baba Buhari
Edita don Allah ka isar min da godiyata ga Maigirma Shugaban kasa game da yadda yake hakuri da ce ce ku cen jama’a. Ina mai godiya a gare shi. Kuma Allah ya ba shi ikon kammala aiki lafiya.
Daga S.M Manager Sabon Gida Jihar Taraba.
Jinjina ga Shugaban kasa
Salam. Gaisuwa da fatan alkairi ga dukkan ma’aikatan jaridar Aminiya. Bayan haka ina mika sakon jinjina ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa manufofin wannan gwannatin na alkairi da fatan Allah ya bai wa shugabanninmu damar cika alkawurar da suka dauka. Amin summa amin.
Daga Ibrahim Khaleel Jama’are. 08059465281.
Kira ga Buhari
Assalam Editan Aminiya da fatan kuna lafiya kira zuwa ga Baba Buhari. Don.Allah ya tuna da mutane ne wadanda ya zo tare da su mafi yawansu, yanzu ba a komai da su.
Daga Abubakar Harande Jihar Sakkwato Shagari (08170823924)
Tunatarwa ga shugabanni
Assalamua alaikum shugabanninmu na Najeriya ku ji tsoron Allah, ku tuna cewa, talakawa suna cikin mawuyacin hali. Don haka ku tuna cewa, kun yi alkawura cewa, za ku yi adalci.
Daga Ni mai son zaman lafiya Aminu 2. Gaye Sankalawa.
Godiya ga Kwankwaso
Gwamnatin Kano bai kamata ku ji haushin taryar da aka yi wa Maigirma Sanata ba. Kowa ya yi da kyau zai ga da kyau. Allah ya taimaki dan Musa Mai gadar sama, mai tituna, mai fitilar kan titi, mai tura yara makarantun kasashen waje. Mun gode dan Musa.
Daga Tahamu Sharef Abdulkareem (Khairan).
A wayar wa jama’a kai game da dimokuradiyya
Tabbas ko shakka babu an fara samun ci gaban dimokuradiyya a nahiyar mu ta Afirka duk da cewa har yanzu jaririya ce ba ta gama girma ba, ganin irin yadda aka fara siyasa ba dauki dora ba duba da yadda aka fara ba talakawa abin da suka zaba, ba tare da magudi ko dauke akwati da dai makamantansu a lokacin gudanar da zabe sai dai kash! da irin halin da al’ummar Jihar Ribas a Najeriya suka dauka na far wa junansu, wai da sunan dimokuradiyya ake yi. Daga karshe nake kira ga ’yan uwana matasa da mu tashi tsaye domin ci gaba da wayar wa al’umma da kai wajen ganin dumokuradiyya ta samu gindin zama a nahiyar mu ta Afirika kamar yadda Turawa ke moriyarta a kasashen su
Daga Naziru Abubakar Sabo Gusau 07033565999 [email protected]