✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Nakasassu ta duniya: Yadda nakasassu ke fuskantar wariya

… Ba ma son yin bara Ranar 3 ga watan Disamba wadda ta yi daidai da Talatar da gabata ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware…

… Ba ma son yin bara

Ranar 3 ga watan Disamba wadda ta yi daidai da Talatar da gabata ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bikin tunawa da nakasassu a fadin duniya kuma an kirkiri bikin ne a shekarar 1992 da nufin fahimtar matsalolin nakasassu da samar da hanyoyin da za a magance su tare da biyan bukatunsu da kuma uwa-uba wayar da kan mutane kan illolin nuna musu wariya.

A ranar 23 ga watan Janairun bana ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a dokar hana wariya ga nakasassu, bayan kusan shekara 9 suna fafutukar neman ta, inda dokar ta hana nuna musu wariya da kuma tanadar da cin tara har da zuwa fursuna ga duk wanda ya karyar dokar. Amma sai dai kusan ana iya cewa har yanzu ba ta sauya zani ba.

Jihar Oyo:

A Jihar Oyo akwai wasu magidanta ’yan uwan juna su uku masu suna Malam Sa’adu Isiaka da Nasir Isiaka da Sulaiman Isiaka da suke zaune a garin Ago-Are cikin Karamar Hukumar Atisbo a Jihar Oyo. Babbansu Malam Sa’ad Isiaka mai shekara 62 ya ce, “kafin ciwo ya kama mu ni Sa’adu ina sana’ar gyaran rediyo, Nasir bakaniken mashin, Sulaiman bakaniken mota. A lokacin da ciwon ya kama mu sai muka yanke shawarar yin amfani da kudin da ke hannunmu wajen sayen wannan injin da ake nikan garin alabo da hatsi. Ba mu taba tunanin fita yawon bara ba, domin wannan abun kunya ne gare mu.

“Akwai ’ya’yanmu da suke karatu a kananan makarantun gwamnati a wannan gari na Ago-Are, wadanda muke daukar dawainiyar karatu da rayuwarsu daga dan abun da muke samu a wannan sana’a. Muna rokon a taimaka mana da injin nika na zamani.”

Jihar Filato:

A Jihar Filato, Wazirin Sarkin Guragun Jos Alhaji Hamisu Bala, ya bayyana cewa idan har gwamnatocin kasar nan za su tallafa wa nakasassu, za su daina yin bara.

Ya ce babban abin da ya kawo matsalar barace-baracen a Arewa shi ne yadda ake mayar da nakasashe koma baya, a ware shi a rika nuna masa bambanci, maimakon a karfafa masa gwiwa.

Jihar Katsina:

Jihar Katsina na da nakassun da suka haura dubu 17 a wata kididdigar tantacewar da har yanzu ake cikin yi. A binciken da Aminiya ta yi, babu wani wuri na musamman da aka kebe a matsayin muhalli kodai a gwamnatance ko daidaikun mutane don kulawa da nakasassu. Duk da cewa akwai wani sashe na hukuma da ke kula da nakasassu. Binciken da muka yi sashen ya fi mayar da hankali a wajen koya wa nakasassun sana’a, musamman guragu da kurame da kuma kadan daga cikin makafi. Matsugunnan da aka fara ba su don koyon sana’o’in sun fara daga Babbar Ruga, suka dawo Kofar ’andaka. Bayan nan aka sake mayar da su a Ma’aikatar NA da ke Kofar Soro, karshe a yanzu suna ma’aikatar SEMA.

Ta fuskar ilimi, za a iya cewa Jihar Katsina ta taka rawar gani a wajen ba nakasassu ilimi. Gwamna Masari yake bayar da gudunmuwa a gwamnatance ga wadannan makarantu da aka raba biyu, wato ta makafi da ke cikin garin Katsina da kuma ta kurame da ke garin Malumfashi.

Shugaban Makarantar Makafin, Malam Lawal Jibrin ya ce, “in ma za a ce akwai wani bambanci a tsakanin wadannan makarantu da sauran bai wuce na nau’ukan kayan aiki saboda lalurar da suke da ita ba. Amma hatta da sabulun wanka ko wanki gwamnatin jiha ke ba su. Ina tabbatar maka babu wani abin da iyayen yaran nan za su ce suna kawowa yaran ta kowace fuska, domin in an yi hutu, kudin motar da za su shiga don komawa gida, a nan ake ba su. Saboda haka, batun bara a Jihar Katsina ina iya cewa, an rage da kashi 80 zuwa 85 a cikin 100.”

Kurosriba:

A Kudu Maso Kudu, galibin ’yan Arewa masu larurar nakasa an fi saninsu da yin bara, amma daga shekarar 200 zuwa ta 2002 jihohin Bayelsa, Ribas da ma Enugu sun rika daukar guragu matsayin wakilansu kuma ’yan jiharsu suna wakiltar jihohin a wasannin motsa jiki na kasa da ake kira NAFEST.

Jihohin Akwa Ibom kuma da Kurosriba sun rika yin amfanin da gurgunta suna tallar yaki da cutar shan inna.

Alhaji Salisu Ali Sale wato SAS, ya shaida wa Aminiya cewa kalubalen da suke fama da shi, shi ne na neman gurbin kara karatu a jami’o’in Kalaba, inda ya ce ban da ta harkar wasan motsa jiki babu wani abin da ke tsakaninsu da gwamnatocin yankin.

Jihar Jigawa:

Galadiman Sarkin Makafin Dutse, Malam Musa Galadiman ya ce gwamnati na yi wa makafi kallon hadarin kaji, inda ya ce babu abin da gwnatin ta tanada musu da za a hana su bara.

Ya kara da cewa makafi a Jihar Jigawa ba su san ana shugabanci a Najeriya ba sai lokacin Buhari, saboda shi ne yake ba makafi da guragu tallafi.

Galadiman ya ce akwai bukatar sauran ’yan siyasa su yi koyi da halayan Buhari wajen tallafa wa nakasassu da ba su aikin yi domin su zama masu dogaro da kansu maimakon a ce suna zama mabarata.

Jihohin Legas da Ogun:

Sarkin makafin Abekuta Malam Yakubu ’Yanleman Hadeja ya ce, “idan akwai abin da ke damunmu shi ne yadda mata lafiyayyu ke zuwa daga Arewa da yara, su zo domin bara, su ne kalubalenmu. Da Allah Ya sa da lafiyata babu abin da zai sa ni bara, don kaskanci ce.” Sarkin Guragun Alagbado, Malam Abubakar Ibrahim cewa ya yi, “dalilin da ya sanya ka ga akwai tarin nakasassu a Unguwar Alablgbu shi ne, saukin kudin hayar gida. A baya can lauya mai kare hakkin dan Adam Cif Gani Fayohemi ne ke biya mana kudin haya, amma tun bayan rasuwarsa babu wanda yake taimaka mana, yanzu haka kudin hayar dakunanmu sun yi tsada fiye da a baya. Sannan akwai matsalar kama mutanenmu, akwai mutanena da aka kama kamar mutum 18, yau sama da shekara 5 har yau babu labarinsu, na yi duk abin da zan iya yi, har mun hakura mun bar wa Allah.

“Sannan akwai mutum biyar da aka kama bayan an sako su saboda tsabar wahala da suka sha duk sun mutu.”

Shehu Isa Dayyanu Dumus, nakasasshe ne da ya ce bai taba bara ba a rayuwarsa. Ya ce ya kamu da cutar kyanda yana dan wata 9 a duniya. “Ina karami mahaifina ya kai mu wajen wata mata makauniya domin ta koya min bara, ni kuma na ki yarda. A haka na yi ta fama mahaifina yana nuna bacin ransa har na shiga garin Kano na shiga makarantar firamare ta Shahuci. Ina zuwa ina yin gadin motocin masu wasan polo a duk ranar Alhamis. Da wannan kudin gadin nake samu abin da nake daukar dawainiyar kaina da na karatuna, daga nan wasu abokaina nakasassu suka kai ni Filin Jirgin Kano. Nan ma na ga su bara suke yi, sai na kama sana’ar wanke takalmi. A nan ne na samu lakanin Fesfes, sai na koma Legas a shekarar 1983, inda na kama shago a Filin Jirgin Murtala Muhammad a Legas.  Yanzu haka halin da nake ciki mahukuntan wajen wato FAAN sun kwace min shagona da sunan za a yi gyara, bayan an gama gyaran duk abokan sana’ata masu lafiya an mayar musu amma ni saboda nakasata sun hana ni wajen neman abincina. Na kai maganar majalisa ta kasa an yi musu sammaci an ba su umarnin su ba ni wajen har yanzu sun yi watsi da maganar bayan makudan kudadena da suka karba.”

Jihar Kano:

Shugaban Kungiyar Kanawa Educational Forum Abba Sarki Sharada ya ce shekara guda ke nan da Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari ya sanya hannu a kan dokar nakasassu amma har yanzu lamarin bai sauya zani ba.

Aminiya ta zanta da Farfesa Jibril Isa Diso, wanda makaho ne, wanda ya ce suna alfahari da wannan rana musamman ganin yadda al’ummar duniya suke ba ta muhimmanci.

Ya yi kira ga ’yan uwansa nakasassu da su nemi ilimi, kasancewar ita ce hanyar da za su samu daraja da kima a idon kowa.

Farfesan ya kara da cewa idan har aka fara aiki da dokar nakasassu, rayuwarsu za ta inganta domin wata rana sai an samu nakasasshe ya rike wani babban mukami a kasar nan kamar yadda ake yi a kasashen duniya.

Malam Saminu Ali wanda ke bara a titin Kofar Kabuga a Jihar Kano, ya bayyana cewa shi bai san da wannan rana ba. “Wanda ke fama da yawon bara na neman abin da zai sa a bakinsa, ina zai san da wata rana da aka bikinta. Gwamnati ta yi watsi da mu ba ta taimaka mana. Amma sai ka ji ana zaginmu wai muna yin bara. To idan ba mu yi bara ba me za mu ci?”

Jihar Kaduna:

Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna Hajiya A’isha Ummi el-Rufa’i ta ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta himmatu wajen inganta rayuwar nakasassu ta hanyar ba su tallafi.

Ta bayyana haka ne a wajen taron Ranar Nakasassu ta Duniya da aka gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A cewarta, nakasassu suna da dogon tarihi a game da kalubalen da suke da shi na rayuwa, wanda a sanadiyyar haka rayuwa ta yi musu tsanani.

Uwargidan Gwamnan ta ce ilimi ya canja tunanin al’umma na daukar masu nakasa a matsayin marasa tasiri a cikinsu. Tun da farko a jawabinsa na maraba, Shugaban Tsangayar Ilimi na Jami’ar Ahmadu Bello Farfesa Yahaya K. Kajuru, wanda Dokta Musa Idris Harbau Shugaban Sashin Ilimi da Tsara Manhajja ya wakilta, ya ce a matsayinsu da huruminsu na bayar da ilimi ga masu nakasa kuma sun jajirce don ganin sun dauki dalibai da suka cancanta ne kawai don yin karatu.

Ya ce za su ci gaba da samar da yanayi da kayan aiki na zamani, domin samar da ingantacciyar koyarwa ga masu lalura.

Shi kuma Sarkin Makafin Gundumar Tudun Wada, Kaduna Malam Bello Abubakar Talata Mafara ya koka akan yadda ya ce ba a dauke su da muhimmanci ba a cikin al’umma. A cewarsa, nakasassu na fama da matsaloli masu yawa a kasar nan tun daga rashin ingantaccen ilimi gare su da kuma ’ya’yansu da rashin kiwon lafiya, wanda ya ce ba su samun saukin kula da su a asibiti, duk kuwa da irin laluran da suke fama da su.

Babban Birnin Taraya Abuja:

Wani matashi mai suna Rabi’u Muhammad na daukar hankalin jama’a da ke ratsawa ta mahadar NNPC a garin Kubwa, a sakamakon yadda yake shigar ’yan hidimar kasa ta hanyar sanya suturarsu. Aminiya ta zanta da shi, ya ce ya yi makarantar boko a matakin firamare da kuma sakandare da ya kammala a shekarar 2014 a Hadeja. Sai dai ya ce matasalar rashin abin hannu ta sa dole ya hakura. Ya ce yakan sanya suturar ce sakamakon sha’awar da yake da ita na ci gaba da karatu.