✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Muhalli ta Duniya: UNICEF za ta shuka bishiyu a makarantun Kano 500

Yara mata sun fi cutuwa domin su ake ɗora wa nauyin ɗebo ruwa don amfanin yau da kullum.

Asusun Tallafa wa Yara na Hukumar Ɗinkin Duniya UNICEF tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin bai ɗaya ta Jihar Kano  SUBEB, za su shuka bishiyu a makarantu 500 da ke faɗin jihar.

Shugaban UNICEF a Kano, Mista Rahama Rihood Mohammed Farah ne ya bayyana hakan albarkacin bikin Ranar Muhalli ta Duniya.

Aminiya ta ruwaito cewa an gudanar da bikin tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin Jihar Kano da suka haɗa da Ma’aikatar Muhalli da Hukumar Ilimin bai ɗaya da Hukumar da ke Kula da Tsabtar ruwan sha da muhalli (RUWASA) wanda ya gudana a Makarantar Sakandiren ‘Yan mata ta Hasiya Bayero.

Mista Rahama ya bayyana cewa UNICEF tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano za su shuka bishiyu a ƙananan hukumomi 7 a faɗin jihar a wani mataki na yaƙi da kwararowar hamada da kuma ɗumamar yanayi.

A cewarsa, ɗalibai a makarantu ne suka fu cutuwa a duk lokacin da muhalli ya samu matsala, ƙasa za ta daina fitar da tsirrai kuma za a samu kamfar ruwa wanda wannan canjin zai shafi rayuwar mutane musamman ma yara ƙanana domin za su fuskanci rashin abinci mai gina jiki da rashin ruwa wanda zai kawo cikas ga ci gaban rayuwarsu.

“Yara mata sun fi cutuwa domin su ake ɗora wa nauyin ɗebo ruwa don amfanin yau da kullum wanda kuma hakan ke iya jefa rayuwarsu cikin hatsarin cin zarafi.”

Mista Rahama ya ƙara da cewa kwararowar hamada da zaizayar ƙasa abubuwa ne da ake samun ƙasar nan musamman ma a Arewacin Najeriya  wanda ke fama da ɗumanar yanayi da kuma samun ƙarancin ruwan sha, lamarin da ya janyo bushewar kadada da samun ci baya wajen sanar da amfanin gona.

A cewar Mista Rahama, UNICEF tana iya ƙoƙarinta wajen yaƙar ɗumamar yanayi  ta hanyar fito da shirye shirye da za su taimaka a wannan fannin.

Ya yi kira ga gwamnati da ta haɗa kai da al’ummomi wajen wayar musu da kai tare da samar musu da kayan aiki yadda za su yaƙi da sauye-sauyen da ake samu na yanayi.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kano cewa suna da rawar takawa wajen ɗaukar matakin gaggawa akan kula da muhallinsu da kuma yaransu a matsayinsu na manyan gobe.

A jawabinsa, Kwamishinan Muhalli Nasiru Sule Garo, ya bayyana cewa yana da matuƙar amfani yara su fahimci irin muhimmanci da ke akwai a sha’anin kula da muhalli tun suna ƙanana domin idan sun girma su taso da son abin a ransu.

“Wannan rana tana da matuƙar muhimmanci musamman ga yara domin su fahimci muhimmanci muhalli ga ɗan Adam.

“Hakan zai sa yaran su taso da sha’awar gyaran muhalli tare da inganta shi ta yadda za a yi maganin matsalolin da yanayi ke ciki na ɗumamar yanayi da kwararowar hamada da gujewa sare bishiyu.

“Muna kira ga yaran da su kula da waɗannan bishiyu su rene su har su fito su girma su amfani al’umma.”

A yayin taron, an shuka bishiyu masu yawa a Makarantar ‘Yan mata ta Hasiya Bayero, inda aka buƙaci malamai da ɗaliban makarantar da su kula da bishiyun don ganin sun girma saboda amfani makarantar da al’umma gaba ɗaya.