✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Hijabi: Fitattun mata da aka yi wa tambari a duniya

Aminiya ta yi waiwaye kan wasu fitattun mata da suka zama jan wuya wajen sanya Hijabi.

A yau Talata da ta yi daidai 1 ga watan Fabrairu, ta kasance ranar da a duk shekara aka rike ta a matsayin Ranar Bikin Sanya Hijabi ta Duniya.

Ranar Hijabi ta Duniya dai ta samo asali ne daga Nazma Khan, wata mata ’yar kasar Bangladesh da ta yi kaura zuwa Jihar New York a kasar Amurka tun ba ta wuce shekaru 11 a duniya ba.

A shekarar 2013 da Nazma Khan ta kirkiri Ranar Hijabi ta Duniya, ta soma wayar wa matan duniya kai ta hanyar sadarwar yanar gizo da a yanzu aka fi sani da intanet, lamarin ya ja hankalin Musulmi da wadanda ba Musulmii ba a kasashen duniya.

An fara bikin wannan ranar ce don jan hankalin matan duniya, wajen suturta jikinsu da kuma kwadaita masu sa hijabi, koda sau daya ne domin gani yadda girmama mace yake a Musulunci.

Alkaluma sun nuna cewa sama da kasashe 140 ne ke raya Ranar Hijabi ta duniya, ta hanyar taron laccoci da fadakarwa a kan fa’idar da ke tattare da sanya hijabi

Daga cikin muhimamn abubuwan da ake tunatar da mata a kansu a wannan rana har wayar da kansu kan muhimmancin da ke tattare da sanya hijabi da tasirinsa wajen kare mutuncin duk wata ’ya mace.

Sai dai galibi Kasashen Yamma da wadansu wadanda ba sa martaba mutuncin ’ya mace, suna sukar Ranar Hijabi ta Duniya da cewa ana muzguna wa mata ta hanyar tursasa musu sanya hijabi musamman la’akari da yadda ya zama wajibi ga wasu matan a kasashen Musulmi irinsu Iran.

Da wannan ne Aminiya ta yi waiwaye a kan wasu fitattun mata da suka zama jan wuya wajen sanya Hijabi duk da kasancewarsu ’yan gwargwamaya a wasu fannoni na rayuwa da kuma shiga wuraren da galibi ake sukar ire-irensu.

Firdausi Amasa

Firdausi Amasa ita ce wacce aka fi sani da macen da ta kwatowa Mata Musulmi ’yancin sanya hijabi a Makarantar Lauyoyi ta Najeriya.

Firdausi Amasa tare da ‘yan uwanta lokacin da aka ba ta shaidar zama lauya

Firdausi Amasa, ita ce matashiyar nan wadda aka ki bai wa takardar shaidar kammala karatun lauya a Makarantar Lauyoyi ta Najeriya saboda ta sanya hijabi a kan kayanta na aikin lauya lokacin da ake bikin yaye lauyoyi a shekarar 2017.

Duk da ta cewa daga bisani ta karbi shaidar zama lauya bayn kwan-gaba-kwan-baya da aka rika yi gami da tayar da jiyoyin wuya da fusata al’umma da lamarin ya yi, a wancan lokaci Firdausi Amusa wadda ta ki ta cire hijabinta, ta ce dole ne ta sanya lulubi sannan ta saka hular lauyoyi a kanta.

Rahotanni sun ce Firdausi ta bayyana matakin a matsayin wani abin da ya keta hakkinta na bil Adama, wanda wannan batu ya mamaye kafofin sada zumunta a ciki da wajen Najeriya tun daga ranar da wannan abun ya faru.

Aisha Yesufu

Aishe Yesufu da wasu ke yi wa kirari da mace mai kamar maza, ta kasance daya daga cikin mutane da suka shafe shekaru suna gwagwarmayar ganin shugabanni sun yi riko da adalci wajen gudanar jagoranci a kasar nan.

Aisha Yesufu a lokacin zanga-zangar EndSARS

Mafi akasari mutane na iya cewa sunanta ya shahara ne a fafutikar #BringBackOurGirls, wanda take daya daga cikin wadanda suka assasa wannan tafiya domin ganin an ceto Dalibai Mata da mayaka Boko Haram suka sace a garin Chibok a shekarar 2014.

Sunan Aisha Yesufu da kuma hotonta sanye da hijbai sun kara yin tashe a lokacin zanga-zangar #EndSARS domin neman kawo karshen cin zalin da ake zargin ’yan sanda da aikatawa.

A yayin da Firdausi Amasa ta ci nasara, fafutikar su Aisha Yesufu ya kai ga rushe rudunar ’yan sandan SARS da ake zargi, a yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kansa ya fito ya yi alkawarin kyautata yanayin aikin ’yan sanda.

Deqa Dhalac

Deqa Dhalac, wata mace ce Musulma ’yar gudun hijira ta zama mace kuma bakar fata ta farko da ta zama Magajin Garin Mainea, wanda kashi 90 cikin 100 na mazaunansa fararen fata ne a kasar Amurka.

Deqa Dhalac, mai shekara 53, wadda ’yar gudun hijira ce daga kasar Somaliya ta zama Musulma bakar fata ta farko a matsayin Magajin Garin da ke yankin South Portland ne bayan shugabannin yankin — wadanda dukkansu fararen fata ne suka zabe ta ba tare da hamayya ba.

Da take jawabi bayan karbar rantsuwar kama aiki a watan Yulin 2021, Dhalac ta ce: “Mutane na da irin ra’ayoyinsu… amma a yau da gobe za su zo su san ko kai wane ne, su saurare ke har su saimaka maka.”

Deqa Dhalac – Magajin Gari mace ta farko a Amurka

A shekarar 1992 ne Deqa Dhalac ta koma kasar Amurka da zama a matsayin ’yar gudun hijira bayan yakin basasa ya barke a kasar Somaliya. Ita ce kuma mutum na farko daga Somaliya da ya zama magajin gari a duk fadin kasar Amurka.

Deqa Dhalac ta bayyana cewa ta shiga siyasa ne saboda kawar muguwar siyasar kyamar Musulunci irin ta tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump.

Ta ce a lokacin da ta fara takara a 2018 wasu mutane tsoro suke ji su bude mata kofa ta shiga gidajensu a yayin da take bi gida-gida domin yakin neman zabe; Wasu ba su ma yi zaton tana iya yin magana da harshen turancin Ingilishi ba.

Don haka ta ce tana alfahari da nasarar da ta samu kuma tana fata zai zama kyakkyawan misali abin koyi ga sauran al’ummomi marasa rinjaye da masu tasowa a kasar.

Bayan zaben ta da aka yi a yankin na Kudu da gabar Maine, kungiyar shugabannin yankin ta ce, “A matsayinta na bakar fata kuma Musulma ta farko a majaliasr shugabannin Portlan, Magajiyar Gari Dhalac babbar jigo ce wajen kawo canji a cikin wannan al’umma.”

Raffia Arshad

A watan Mayun 2020 ne aka nada Raffia Arshad a matsayin alkali a kotun kasar Birtaniya, lamarin da ya sanya ta zama Musulma kuma mai sanya hijabi ta farko da ta taba samun wannan matsayin Birtaniya.

Raffia Arshad ita ce Musulma da ke sanya hijabi ta farko da ta taba zama alkali a Birtaniya.

Raffia Arshad wacce a yanzu ta shekara 42 a duniya,  ta zama alkali a yankin Midland bayan shafe shekara 17 tana aikin shari’a.

Ita ce alkali mai sa hijabi ta farko a Birtaniya
Raffia Arshad ce alkali mai sa hijabi ta farko a Birtaniya.

Bayanai sun ambato Raffia tana shaida wa manema labarai cewa a baya ta dauka matsayin iyayenta da kasancewarta daga al’umma marasa rinjaye za su zama mata kalubale a fannin sharia.

A wancan Raffia Arshad ta ce, “Wannan nasarar ba tawa ba ce ni kadai. Nasara ce ga dukkan mata musamman Musulmai, har ma da wadanda ba Musulmai ba,” inji ta.

Raffia ta yi alkawarin amfani da sabon matsayinta wurin yin adalci da bayar da murya ga kowane bangare.

Ta bayyana yadda takwarorinta masu sanya hijabi suka mara mata baya a matsayin abin da ya fi faranta mata rai game sabon matsayin nata.

“Mutane da dama, maza da mata sun yi ta aiko mini da sakon taya murna.

“Wadanda suka fi daukar hankalina su ne mata masu hijabi da a baya suke ganin ko lauya ba za su iya zama ba, ballantana alkali,” a cewarta.
A shekarar 2004 Alkali Raffia ta fara aiki da ofishin shari’a na St Mary’s Family Law Chambers.

A shekaru 17 na aikinta a fannin ta samu gogewa a Shariar Musulunci, hakkin yara, cin zarafi da kuma auren dole.

Sai dai ta ce duk da haka ta fuskanci nau’uka tsangwama. Ta bayyana yadda a wani lokaci wani akawun kotu ya yi mata kallon mai aikin tafinta a cikin zauren kotu.

Shatu Garko

Shatu Garko, wata matashiya ’yar Jihar Kano ita ce ta lashe Gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta shekara ta 2021 da ka gudanar.

Matashiyar ita ce mace ta farko mai sanya hijabi da ta taba zama sauraniyar kyau a kasar nan.

Haka kuma Shatu Garko mai shekara 18, ita ce kadai mace mai sanya hijabi da ta shiga gasar wadda ta lashe a matsayin wadda ta wakilci yankin Arewa maso Yamman Najeriya a gasar.

Shatu Garko Sarauniyar Kyau
Shatu Garko- Sarauniyar Kyau ta Najeriya, kuma mai sanya hijabi ta farko da ta zama Sarauniyar Kyau a Najeriya

A ranar Juma’a 17 ga watan Disamba, 2021, ne aka sanar da Shatu Garko a matsayin sabuwar Sarauniyar Kyau, bayan Etsanyi Tukura, daga Jihar Taraba da ta lashe gasar karo na 43 a 2019.

Kyaututtukan da ta samu na lashe gasar sun hada da kudi Naira miliyan 10 da sabuwar mota sannan za a kama mata daki na tsawon shekara daya kyauta a wani katafaren otal.

Amniya ta ruwaito an gudanar da gasar ta bara a Cibiyar Landmark da ke Ungwar Victoria Island a Legas, wadda ita ce karo na 44 da aka gudanar da ita a Najeriya.