Dalibai mata Musulmi a makarantar sakandare mallakar Jami’ar Ibadan sun samu ’yancin sanya hijabi a tare da kayan makarantansu.
Alkalin Babbar Kotun Jihar Oyo, Mai Shari’a Moshood Ishola, ne ya yanke hukuncin halasta wa daliban sanya Hijabi.
Ya soke haramcin sanya hijabi da hukumar gudanarwar makaranta ta yi ne a zaman sauraron karar da ya yi a ranar Laraba a Ibadan, babban birnin jihar.
Alkalin, ya ce ya danganta hukumcinsa ne da irin wannan shari’u da aka yanke hukuncinsu a baya a Kotun Koli.
Ya ce ya yi amfani da dokokin kasar Najeriya da suka amince wa addinai da kungiyoyi ’yancin cin gashin-kai.
Alkali Ishola ya ce hukumar wannan makaranta ko wani ma’aikacinta ba su da ikon hana daliban ’yancinsu na addini kamar yadda dokokin kasa suka tanadar.
Saboda haka ya umarci hukumar makarantar ta kyale dalibai mata Musulmi su ci gaba da sanya hijabi.
Rikicin sanya hijabi a makarantar ta faro ne cikin watan Nuwambar 2018 a lokacin da hukumar makaranta ta hana dalibai Musulmi sanya hijabi.
Hakan ne ya sa daliban da iyayensu suka maka makarantar gaban kuliya domin a kwato masu ’yanci.