Ranar 26 ga Agustan kowace shekara ita ce ranar da aka kebe a matsayin Ranar Hausa ta Duniya. An sanya wannan rana ce don ta yi daidai da ranar da masana suka kirkiro haruffan K da D da suaransu. A bana an gudanar da wannan taro a ranar Litinin da ta gabata inda al’ummar Hausawa da jami’o’i a fadin duniya suka gudanar da bukukuwa don munar zagayowar wannan rana wacce aka ba taken “Kalubalen Hausa da Hausawa.” Aminiya ta jin ta bakin masu ruwa-da-tsaki a bangaren harshen Hausa daga sassasa daban-daban na Arewacin kasarnan kamar haka:
A Jihar Kano Kungiyar Dalibai ta Jami’ar Bayero da hadin gwiwar Sashen Koyar da Harsunan Najeriya na Jami’ar sun gudanar da irin wannan taro inda masana suka gabatar da makaloli a kan harshen da kuma irin alfanunsa.
Farfesa Abdulkadir Dangambo Malami a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya na Jami’ar Bayero ya yi wa Aminiya karin haske game da muhimmancin wannan rana inda ya ce, ranar za ta samar da hadin kai a tsakanin manazarta Harshen Hausa da sauran Hausawa “Haduwar Hausawa da manazarta a wuri daya don bikin wannan rana zai zama wani abu da zai samar da hadin kai a tsakaninsu don bunkasa harshen. Su manzarta su ne ke gudanar da bincike wanda kuma za su iya isar da sakamakon bincikensu cikin sauki har a samu sauran Hausawa su yi amfani da binciken wajen bunkasa harshen,” inji shi.
Farfesa DanGambo ya bayyana cewa ranar da aka ware ta zamo nasara kuma hakan ya kara daukaka darajar harshen Hausa a idon duniya.
Dokta Abdulkadir Labaran Koguna, shi ne Shugaban Kungiyar Al’ummar Hausawan Afirka ya shaida wa Aminiya tarihin wannan rana ta duniya inda ya ce ranar ta samu ne bayan binciken da kungiyarsu ta gudanar inda ta gano Mista Hans Bischer, wanda aka fi sani da Dan Hausa ya kirkiro haruffan k da d da b a ranar 26 ga watan Agustan1912, don haka aka dauki ranar ta zama Ranar Hausa ta Duniya. “Kin san a jami’o’i da sauran manyan makarantu ana shirya makon Hausa. To sai muka fuskanci cewa wannan taron yana tsayawa ne iyakar wadanda ke jami’a kadai ke halarta, don haka muka yi tunanin samun wata rana guda da kowane Bahaushe zai iya zuwa wurin. Sai muka yanke shawarar a dauki ranar da Dan Hausa ya kirkiro haruffan Hausa na K da D da B wadanda babu su a jerin rubutun boko. Mun fara wanan taro ne a shekarar 2015 a Abuja,” inji shi.
A cewar Dokta Koguna a yanzu haka fiye da kasashe 40 inda al’ummar Hausawa suke a Afirka sun karbi wannan rana tare da gudanar da bikin a kowace shekara a wannan rana “Alhamdulillah a yanzu kusan dukkan kasashen da ke Afirka inda Hausawa suke sun karbi wannan rana haka kuma muna amfani da take guda. Kamar a bana dukkan kasashen mun yi amfani da taken “Kalubalen Hausa da Hausawa,” inji Dokta Koguna.
Da yake bayani game da kalubalen da Harshen Hausa ke fuskanta Dokta Abdulkadir Koguna ya ce a yanzu babban kalubalen da harshen ke fuskanta shi ne yadda wadansu ke yi wa kutse wa harshen musamman a tallace-tallacen Hausa. Ya ce, “Yanzu idan kika dauki yadda ake yin tallace-tallace da harshen Hausa a kafafen watsa labarai abin takaici ne. Akwai wani talla da na gani an rubuta “Allah Ya yi aure da marar kwabo.” Muna nan muna kokarin ganin Kungiyar AFCON ta tsaya tsayin daka wajen ganin an gyara wannan matsala.” Haka kuma ya ce, “Harshen Hausa na fuskantar kalubalen da aka mayar da shi raba-danni a cikin darussan da ake koyar da daliban kimiyya. Yanzu an sanya cewa daliban kimiyya ba su karanta harshen Hausa a makaratun sakandare an mayar da harshen ya zama raba-danni. Sai ka ga yaro Bahaushe ya gama sakandare amma bai iya rubutun Hausa ba,” inji shi.
Farfesa Ango Abdullahi, ya shaida wa Aminiya irin muhimancin da harshen uwa yake da shi inda ya ce, “Harshen Hausa na da matukar muhimmanci domin kowane dan Adam harshen da yake magana da shi da harshen da aka haifeshi da shi suna da muhimmanci kwarai da gaske gare shi kuma harshensa yana tare ne da ci gaban kasarsa da ci gaban rayuwarsa. A yau ku duba dukkan kasashen duniya da kyau ba wata kasa da ta ci gaba da kayan aro, ka san Hausawa dama suna cewa kayan aro ba ya rufe katara, ka ga a nan mu da muka aro harshen Ingilishi da shi ne wai za a gina kasa, wannan yana da wuya, ka duba da kyau Indiya suna da harshensu rubutacce, haka kasar China da sauran kasashe. ko da an mulke su a da za ka tarar sun koma harshensu na asali, kuma da shi suke tinkaho kuma suke gina kasa. Yau in ana maganar kasashen da suka ci gaba dole kasar China tana gaba, Japan tana gaba Indiya ma tana gaba, ka san kuwa kasar Indiya Turawa sun mulke ta sai da suka yi shekara 300 suna mulkin Indiya. Amma ta koma harshenta da shi take rubutu da shi take komai,” inji shi.
Ya ce, “Na je kasar China shekarun baya sai aka kai ni sashen da ake koyar da Hausa na ji mamakin yaran da suka kewaye ni suna yi min Hausar da ta fi tawa dadi. Ka san Hausar da ake rubutu da ita ita ce Hausar Kano, sai na tambayi daya daga cikinsu wata yarinya na ce mata kin taba zuwa Najeriya? Ta ce a’a. A ina kika koyi Hausa ta ce a nan ga ajin nan da nake koyo ga kuma farfesan da yake koya mana Hausa, saboda sha’awa da na dawo na roka aka kawo su su bakwai zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya suka yi karatun digiri na biyu a Harshen Hausa, kafin su koma kasarsu sai suka zo gidana suka tambaye ni yaya sunan mahaifiyarka da na fada musu sunan mahaifiyata sai daya daga cikinsu ta ce to ita sunan da za ta yi amfani da shi ke nan in ta koma gida.
Dokta Bashir Abu Sabe, Malamin Harshen Hausa ne a Jami’ar Al-Kalam da ke Jihar Katsina, ya bayyana cewa, “Wannan biki ya samu karbuwa a idon duniya inda har Majalisar ta Dinkin Duniya ta ga ya dace ta kebe wata rana wadda ta kira da ‘Ranar Harshen Hausa ta Duniya.’ Wannan ya kara nunawa a fili cewa Hausa ta karbu a duniya,” inji shi.
Dokta Bashir ya kara da cewa, yana da kyau yanzu a bullo da wani tsari ko dokar da za ta bayar da damar a rika karantar da dalibai wasu manyan darussa a Harshen Hausa. “Lokacin da na je Masar karatu, komai da harshen Larabci suke koyarwa hatta ita Hausar, sai dan abin da ba a rasa ba. Koyarwa a cikin harshen uwa yana da matukar muhimmaci, kuma shi zai sa daliban ilimli su kara fahimtar abin da ake koyar da su,” inji shi.
Hauwa Muhammad Bugaje, Malama ce a Sashin Harsuna da Al’adun Afirka a Tsangayar Fasaha da ke Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, ta ce “Dalilin wannan rana ta Harshen Hausa da ake gudanarwa a duk fadin duniya shi ne ciyar da Harshen Hausa gaba, musamman Hausawa da masu kishin Harshen Hausa.
Da farko shi ne al’ummar duniya masu jin Harshen Hausa da wadanda ba sa jin harshen su fahimci matsayin da Harshen Hausa ke da shi a duniya.
Harshen Hausa dai shi ne harshe na 11 wajen masu magana da shi a cikin harsuna 6,500 da ake da su a duniya.
Kuma wannan kididdiga ba wai Hausawa ne suka yi ta ba, masu kula da al’amuram harshe na kasashen Turai ne suka yi kididdigar suka fitar da sakamako.
A fadin Afirka babu wani harshe da ya kai Harshen Hausa matsayi, hasali ma harsunan da ake ganin kamar sun kai bantensu a duniya, kamar harshen Jamusanci, da sauran harsuna duk ba su kai Harshen Hausa ba.
Sannan muna so al’umma su san cewa shi ci gaba ba ya yiwuwa da kayan wani, domin har yanzu kasashen Afirka muna amfani ne da harshen Ingilishi da Faransanci a matsayin harshenmu, alhali kasashen da ba su kai mu ba suna amfani da harsunansu wajen ci gaba. Mu kuma muna amfani ne da harshen ’yan mulkin mallaka, kuma harshen ’yan mulkin mallaka har yanzu yana ba mu wahala don haka ya zama wajibi mu dawo namu harshen.
Duk kasar da ta rungumi al’adunta tana saurin ci gaba domin za mu iya fahimtar haka a kan kasar China da Japan da Saudiyya da saurasu. Don haka mu ma ya kamata mu zama cikkakkun masu ’yanci.