Rundunar Sojin ƙasar Columbia ta tabbatar da cewa fararen hula sun yi garkuwa da dakarunta guda 57.
Janar Federico Alberto Mejía na Rundunar ya sanar a ranar Lahadi cewa mutane kimanin 200 sun yi garkuwa da sojojin ne bisa umarnin ’yan tawayen FARC da suka addabi ƙasar.
Ta bayyana cewa al’ummar ƙasar suna fuskantar matsin lamba daga ’yan tawayen masu ɗauke da makamai.
Sanarwar ta ƙara da cewa an sace sojoji 31 a ranar Asabar, ragowar kuma ranar Lahadi.
- Matashi ya yi wa maraya ɗan shekara 10 kisan gilla a Zariya
- Amurka ta roƙi China ta sa baki kada Iran ta rufe mashigar tekun Hormuz
Erik Rodríguez ya bayyana cewa sace sojojin na da alaƙa da kama wani jagoran ’yan tawayen kungiyar EMC da sojojin suka yi.
Ya ce a yayin da suke ƙoƙarin daukar sa a jirgi ne mutanen suka yi musu ƙawanya suka yi awon gaba su a yankin Kudu maso Yammacin Micay Canyon mai tsaunuka.
Ƙungiyar ’yan tawayen FARC ta addabi yankin Kudu maso Yammacin ƙasar, wanda ya yi ƙaurin suna wajen safarar miyagun ƙwayoyi a kusa da Lardin El Plateado.
Yankin ya yi fice wajen sarrafawa da safarar horar iblis, kuma yana cikin yana daga cikin wuraren da suka fi dama da tashin-tsahina a ƙasar ta Columbia.
A baya kungiyar ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar a shekarar 2016.