✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ranar Hausa: Sai an rungumi Hausa Arewa za ta ci gaba —Masani

 Wani masanin tarihi na kasa a Gidan Adana Tarihi na Arewa House da ke Kaduna, Malam Rabi’u Isa ya ce muddin yankin Arewacin Najeriya na…

 Wani masanin tarihi na kasa a Gidan Adana Tarihi na Arewa House da ke Kaduna, Malam Rabi’u Isa ya ce muddin yankin Arewacin Najeriya na son samun ci gaba, to dole ya rungumi harshen Hausa a matsayin yaren sadarwa a hukumance.—

Ya ce Hausa ne harshen gama-garin ga kusan dukkan kabilun yankin wajen sadarwa da sauran mu’amalar yau da kullum, wanda hakan ya sa ya cancanci zama yaren yankin a hukumance.

Masanin tarihin ya bayyana hakan ne yayin gabatar da makala a taron da wata kungiya mai suna ‘Manufarmu Al’ummarmu,’ ta shirya a garin Jos, Jihar Filato domin murnar zagayowar Ranar Hausa ta Duniya a ranar Laraba.

Ya ce, “Hausa na da banbancewa tsakanin jinsin kowanne abu; Shi ne yare mafi sauki a duniya kuma ya fantsama zuwa kasashen duniya da dama musamman a yankin Yammacin Afirka.

“Akwai sama da mutane miliyan 70 da ke amfani da yaren. A yau, littattafai masu tsarki irinsu Alkur’ani da Baibul sun fi sauki da dadin fassarawa da Hausa fiye da kowane yare a Najeriya”, inji Malam Rabi’u.

Masanin tarihin ya kara da cewa saukin harshen Hausa ne ya sa lokacin da turawan mulkin mallaka suka zo Najeriya ba su fuskanci tangarda sosai ba, haka ma masu wa’azin yada addinin Kiristanci a arewa.

Sai dai ya ce duk da wadannan abubuwan, yaren na fuskantar barazanar kutse daga sauran manyan yarukan duniya.

Shi kuwa shugaban kungiyar da ta shirya taron na ‘Manufarmu Al’ummarmu,’ Abdulmajid Lawal, ya ce la’akari da yadda ranar ke kara samun tagomashi ne ya sa suka ce su ma ba za a bar su a baya ba a bana.

“Hakika harshen Hausa ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa zaman lafiya da ci gaba tattalin arzikin Najeriya”, inji Abdulmajid.