✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Alhamis za mu shiga Kasar China binciko musabbabin bullar Coronavirus — WHO

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa, za ta tura wata tawaga ta kwararru zuwa Kasar Sin domin binciko ainihin dalilin da ya janyo…

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa, za ta tura wata tawaga ta kwararru zuwa Kasar Sin domin binciko ainihin dalilin da ya janyo bullar cutar Coronavirus tun fil azal.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwar da shugaban WHO, Tedros Adhanom ya fitar a ranar Litinin.

Tedros ya ce ayarin kungiyoyin masana a fannin kimiyyar lafiya da suke karkashin WHO kimanin guda 10 ne za su kai ziyara Kasar China a ranar Alhamis 14, ga watan Janairun 2021 don binciko ainihin sabubban bullar annobar COVID-19.

Ya yi ikararin cewa a baya Gwamnatin Kasar ta China ta dakatar da tawagar shiga kasar, sai dai a yanzu ta yi amanna inda Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar ta fidda sanarwar cewa Gwamnatin China za ta baiwa kwararrun duk wani goyon baya yayin gudanar da bincikensu.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Zhao Lijian ta ce za a bukaci tawagar jami’an WHO su killace kansu na tsawon makonni biyu gabanin su shiga kasar domin a tabbatar basa dauke da kwayoyin cutar.

Hukumar ta WHO ta ce tana da burin gudanar bincike na hadin gwiwa da Jami’an lafiya na kasar China domin gano musabbabin cutar ta COVID-19.