✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ranar Alhamis za a yi Sallah — Sarkin Musulmi

Idin karamar Sallah za ta kama ranar Alhamis.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ba da sanarwar rashin ganin watan Shawwal a yammacin ranar Talata, 29 ga watan Ramadan.

Sultan na Sakkwato ya bayyana hakan ne cikin wata takarda da aka raba wa manema labarai a fadarsa da ke birnin Shehu.

Takardar da ke dauke da sa hannun mai baiwa fadar shawara kan harkokin addini kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, ya ce a duk fadin Najeriya ba a samu labarin ganin watan Shawwal ba, saboda haka Ramadanan bana zai cika kwanaki 30.

Takardar ta bayyana Sarkin Musulmi na yi wa al’umma fatan alheri da neman ci gaba da yiwa kasa addu’a.

A wannan sanarwar da aka fitar ya nuna Sallah karama za ta kasance ranar Alhamis, 1 ga watan Shawwal na shekarar 1442 bayan Hijira wacce ta yi daidai da ranar 13 ga watan Mayun 2021.

Tuni dai wasu kasashen musulmai na duniya suka ba da umarnin cike azumin bana zuwa 30, kamar yadda kasar Saudiyya ita ma ta ba da umarni.