✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rana ba ta karya: Ranar sake bude sufurin kasa da kasa a filin jirgin saman Kano ta zo

“An yi duk shirye-shiryen da suka kamata, an girke jami’an tsaro tun ranar Asabar.

Mutane na cike da doki a Filin Sauka da Tashin Jiragen Sama na Malam Aminu da ke Kano kasancewar ranar Talata, 6 ga watan Afrilun 2021 ne za a dawo da sufurin kasa da kasa bayan shafe tsawon lokaci.

A baya dai Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar Litinin, 5 ga watan Afrilu a matsayin ranar bude bangaren, amma daga bisani aka kara matsawa da ita zuwa Talata, saboda Litinin din ta zo a daya daga cikin ranakun bukukuwan Ista.

Wani ma’aikacin filin wanda bai amince a ambaci sunansa ba ya ce wani jirgin saman kamfanin Ethiopian Airline ne zai fara sauka kuma ya debi wasu fasinjojin da zarar an bude.

“A ranar Laraba ma muna sa ran wani jirgin na Egypt Air shi ma zai sauka, amma ba mu san abin da zai iya faruwa kafin nan da goben ba,” inji shi.

Sai dai wasu ma’aikatan a filin jirgin sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi a kan ranar dawowar, yayin da wasu daga cikinsu suka ce har yanzu suna cike da shakku.

Wani daga cikinsu ya ce, “An yi dukkan shirye-shiryen da suka kamata, an girke jami’an tsaro a sabuwar tashar sauka da tashin jirage tun ranar Asabar. Zuwa ranar Lahadi kuwa, an kunna dukkan fitilun wurin, amma dai ba zan iya cewa komai a kan saukar jiragen ba.”

Wakilinmu ya lura cewa sabuwa da tsohuwar tashar sauka da tashin jiragen sama ta kasa da kasa a filin jirgin sun zama tamkar kufai yayin da mutane tsiraru ne suke kaiwa da komowa ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.