Mutum 11 sun rasu a wani harin ramuwar gayya da dakarun hadin gwiwar kasashen Larabwa suka kai wa ’yan tawayen Houthi a kasar Yemen da suka kai hari a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Shaidu da jami’an lafiya sun tabbatar da mutuwar mutanen da cewa dakarun hadin gwiwar sun kai harin ramuwar gayyar ce a Sanaa, babban birnin kasar Yemen, da ke hannun mayakan na Houthi.
- Matar Aure: Rahama Sadau za ta saki sabon shirin mai dogon zango
- Mutum 26 sun rasu a gida daya a girgizar kasa a Afghanistan
Wani wanda aka kashe wa ’yan uwa a harin, Akram al-Ahdal, ya ce, “Mutum 11 sun rasu, ana kuma ci gaba da neman wadanda suka makale a cikin baraguzan gini.”
An kai farmakin ne a ranar Talata kan wasu gidaje biyu bayan harin da mayakan Houthi suka kai ranar Litinin.
’Yan Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran ne suka yi ikirarin kai harin na ranar Litinin a kan birnin Abu Dhabi, hedikwatar UAE, suka kashe mutum uku tare da jikkata wasu shida.
’Ya tawayen Houthi sun sha kai hare-hare kan kasar Saudiyya, amma wannan ne karon farko da ta kai hari a UAE.