Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya sanar da rubanya wa ma’aikatan wucin gadi a Jihar albashinsu har sau uku albarkacin watan Ramadan.
Karin dai zai shafi dukkan ma’aikatan wucin gadi da ke daukar albashin N10,000 a wata.
- NAJERIYA A YAU: Yadda dabino ya zame wa mazauna Kudancin Najeriya zuma
- Shin ya dace a kaurace wa zabe idan gwamnati ta gaza magance matsalar tsaro?
Gwamnan ya sanar da karin ne lokacin da ya jagoranci duba rabon kudi da kayan abinci ga ma’aikatan a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Maiduguri a ranar Litinin.
Ya ce, “Ina alfahari da dukkanku saboda yadda kuke jajircewa a aiki da kuma tabbatar da tsafta da gyaran Gidan Gwamnati.
“Wannan watan Ramadan ne, kuma kamata ya yi duk wata kyautatawa ta fara daga gida, wannan ne ma dalilin da ya sa na yanke shawarar tallafa muku da abinci da wasu ’yan kudade don ku taimaki iyalanku a wannan watan mai albarka,” inji shi.
Gwamnan ya kuma roke su da su yi amfani da watan wajen yin addu’ar dawowar zaman lafiya a a Jihar da ma kasa baki daya.