Watan Ramadana wata ne da Musulmin duniya kan yi ibada ta musamman, wato azumi, a cikinsa.
Yayin azumin Ramadana, sharadi ne a kan dukkan Musulmin baligi kma lafiyayye mazaunin gida ya kame baki daga ci da sha da sauransu tun daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana.
- Ba don jajircewar Buhari ba da matsalar tsaro ta fi haka muni —Ayade
- ’Yan bindiga sun fitar da hotunan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna
Yayin da wadansu masu azumi suka zabi cin abinci mai gina jiki don samun kuzari, wasu kuwa sun zabi yin amfani da abin sha mai bai wa jiki karsashi, kamar ruwan rayuwa gishi da sukari na ORS da makamantansa.
Ruwan rayuwa, kamar yadda ake kiran shi, hadi ne na sinadarai da akan bai wa mara lafiya, musamman ga mai fama da gudawa domin kore masa kasalar da yake ji a jikinsa.
Ana samun shi ne a shagunan sayar da magunguna ba tare da wata doka ko shaidi daga wajen likita ba.
Binciken wakilanmu ya gano cewa, galibin matasa a Kano sun rungumi dabi’ar yin Sahur da kuma buda-baki da ruwan rayuwa, ba don komai, sai don samun karfin yin azumi da kuma aiwatar da ayyukansu a lokacin azumi.
Mariya Sani na daya daga cikin matasan da suke amfani da ruwan rayuwa a lokaci na azumi, ta shaida wa wakilinmu cewa, yin hakan shi ne mafita ga mai yin azumi ba tare da wata wahala ba.
Ta ce, “Ni tela ce, nakan yi amfani da karfin jikina ne wajen yin aiki, wannan ne dalilin da ya sa nakan yi Sahur da buda-baki da ruwan rayuwa don in samu karfin yin aiki. Kasala za ta dame ni sosai idan ban sha ruwan ba.”
Kamar Mariya, ita ma Hadiza Sule ta yi ammanar cewa shan ruwan rayuwa ne mafita wajen samun karfin jiki a Ramadana.
Ta kara da cewa, “Na san likitocin da kan rubuta wa marasa lafiya su yi amfani da ruwan rayuwa saboda rashin kuzari, kuma tun da jiki kan ji kasala da azumi shi ya sa nake shan ruwan don maido da karsashin jikina.
“Ko a makon jiya, bayan da wani yarona ya dawo daga Islamiyya sai ya ce mini in saya mishi ruwan rayuwa ya sha don ya samu karfin cika azumin wannan rana.”
Wakilan namu sun gano cewa, abu ne da aka saba ji da kuma gani a Kano yara su rika neman iyayensu su saya musu ruwan rayuwa don su sha su samu karfin yin azumi.
A nasa bangaren, Muhammad Yusuf ya ce, yana amfani da ruwan rayuwa ne saboda ya san babu wata illa a tattare da hakan.
“Na dauki tsawon lokaci ina amfani da ruwan rayuwa a ciki da wajen Ramadana kuma ba ya yi mini illa.
“Idan a cikin azumi ne, a lokutan Sahur da buda-baki kawai nakan sha ruwan don samun kuzarin jikina,” in ji Yusuf.
Wani mazaunin Kano kuma masanin hada magungunan, Yahaya Muhammad Sani, ya ce an samu karuwar yin amfani da ababen sha masu kara wa jiki kuzari musamman idan aka yi la’akari da yawan jama’ar da kan ziyarci kemis-kemis don sayen wadannan abubuwa a wannan lokaci na azumi.
Yana mai cewa, “Mukan saida katan daya a cikin mako guda a wannan lokaci, amma kafin Ramadana da kyar mu sayar da kwaya 10.”
Shan sa barkatai na da illa —Masana
Sai dai, a matsayinsa na masanin hada magunguna, Sani ya ce shan ruwan rayuwa barkatai ka iya yi wa mutum illa.
“Akwai matsala a tattare da shan ruwan rayuwa barkatai ba tare da umarnin likita ba.
“Wadanda suka manyanta ko masu fama da wani rashin lafiya, sun fi fuskantar hatsarin fama da matsaloli saboda shan ruwan rayuwa.
“Don haka, mutane su rungumi dabi’ar shan asalin ruwa a maimakon ruwan rayuwa.”
Ya kara da cewa, masanin hada magunguna ba zai iya hana sayar da ruwan rayuwa barkatai ba, saboda a cewarsa, “Idan ma ka ki sayar musu da shi, za su tafi wani wurin su saya.”
Da take tofa albarkacin bakinta kan wannan batu, Naseeba Babale, wadda jami’ar kimiyya ce, na ra’ayin duk mai amfani da ruwan rayuwa barkatai ba zai kare lafiya ba.
Ta ce, “Akan ba da ruwan rayuwa ne ga marasa lafiyan da suka rasa abin da ake kira ‘electrolytes’ a jikinsu walau ta dalilin gudawa ko amai.
“Duk da dai jama’a kan yi fama da kishi lokacin azumi, amma ba ya kaiwa ga rasa ‘electrolyte’ a jiki. Saboda ruwan rayuwa na kunshe da gishiri wanda jikin mai azumi ba ya da bukata.
“Ya kamata mutane su yi hattara da shan ORS saboda hakan ka iya haifar da yawan sinadarin ‘sodium’ ga jiki wanda a karshe sai ya haddasa matsalar hawan jini.”
Shi ma likita Abdullah Shittu, ya nuna akwai bukatar jama’a su guji yin amfani da ORS barkatai, “Musamman ga wadanda girma ya kama su ko masu fama da lalurar hawan jini.”
Ba haramun ba ne —Malamai
Wani malami da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa babu wata karantarwa da ta nuna rashin kyawun shan wani abin sha kamar ruwan rayuwa a lokacin azumi.
Yana mai cewa, “An bukaci Muslimi su ci abinci da kyau a lokacin Sahur, an kuma bukaci su jinkirta Sahur din don ba su damar cin abin yadda ya kamata.
“Muddin dai ba a cikin lokacin azumi aka sha ruwan ba, shan shi ba ya bata azumi. Allah ne Masani.”
A nasa ra’ayin, Dokta Shuaibu Doury ya ce matsawar dai abin shan bai kunshi giya ba kuma an kiyaye ba a sha shi lokacin da azumi ke gudana ba, hakan ba ya bata azumi.
“A nawa ra’ayin, zan iya bai wa mutanen da suke aikin karfi da wadana aiknsu ya shafi wasa kwakwalwa shawara a kan yana da kyau su rika shan ruwan rayuwa,” in ji Doury.
Sai dai, tsohon Shugaban Majalisar Malamai na Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, cewa ya yi duk da dai hakan ba haramun ba ne amma ya yi gargadin a daina shan ruwan barkatai ba tare da izinin likita ba
Ya ce, “Tun da dai likitoci ne kan bai wa marasa lafiya damar shan ruwan don samun karfin yin azumi, shan ORS ba ya bata azumi.
“Haka nan, idan likita ya ba da damar shan ruwan rayuwa saboda tsananin zafin rana don a samu saukin yin azumi, babu laifi a cikin haka.
“Ba yunwar da akan ji ne azumi ba, face kamewa daga ci da sha. Idan ka sha ruwan rayuwa don ka samu kuzarin aiwatar da aikinka bai bata maka azumi ba; shan ruwan rayuwa ba haramun ba ne.”
Daga nan, Sheikh Khalil ya buga misali da matar da aka yi mata izinin “Ta sha maganin tsayar da haila domin samun damar yin azumi ko Hajji.
“Da wannan, ba laifi ba ne ka sha ruwan rayuwa don samun karfin yin azumi ko aiwatar da aikinka.”
Bugu-da-kari, Dokta Ibrahim Siraj wanda malami ne a jami’a ya ce, muddin dai Musulunci bai haramta sha ba, to, ba za a hana mutane yin amfani da shi ba.
“ORS ba ya kunshe da wani abu da aka haramta a Musulunci; saboda haka ba za a ce ya haramta a sha shi ba.
“Idan kuwa ya kasance yana kushe da haramun, malamai za su ba da fatawa a kan haramcinsa.
“A nan, malamai za su dogara ne da ra’ayin likitoci wajen ba da fatawarsu.
“Babu matsala a yi amfani da shi muddin likitoci suka amince da hakan.
“Amma idan suka nuna akwai matsala idan aka sha ruwan rayuwan, dole a bi ra’ayin masana,” a cewarsa.