✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: An karya farashin kayan abinci a Katsina

Za a sayar da buhun masara da dawa da gero a kan N20,000 kowannensu

Gwamnatin Katsina da hadin gwiwan kananan hukumominta 34 sun karya farashin kayan abinci albarkacin watan Ramadan mai kamawa.

A ranar Litinin ko talata ake sa ran fara azumin Ramadan na bana, don haka, a ranar Lahadin nan  za a fara neman jinjirin wata, bisa umarnin Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar.

Saboda haka ne gwamnatin Katsina ta ware Naira biliyan gomna domin  sayen hatsin da za su sayar wa masu karamin karfi a farashi mai rahusa a cikin watan azumin.

Sakataren yada labaran gwamnatin jiharIbrahim Kaula Mohammed, ya sanar cewa za a rika sayar da buhun masara, dawa da gero a kan N20,000 kowannensu.

Amma a cewarsa, domin tabbatar da adalci da ganin kowa ya samu, ba za a sayar wa mutum guda fiye da kwano 10 ba.

A cewarsa, iyalai 400,000 ne ake sa ran za su amfana da abincin mai saukin farashi, sai kuma gajiyayyu da tsofaffi 33,000 da za su samu tallafin abinci da kudade daga gwamnati.

An kafa kwamitocin sayar da hatsin da kuma rabon abincin buda baki a matakin jiha karkashin jagorancin Mallam Khalil Musa Kofar Bai, sai kuma wakilan kananan hukumomi.

Aikin kwamitin ya hada da gudanarwa da kuma tabbatar da ingancin girki da kuma adalci a rabon abincin buda bakin gami da tura kudaden hatsin da aka samu zuwa asusun gwamnati.

A cewarsa, gwamnatin jihar na da nufin ciyar da iyalai 72,000 a kowace rana a cikin watan Ramadan, wato jimillar mutane miliyan 2.1.

Don haka kwamitin kananan hukumomi zai sa ido kan sayar da hatsin da kuma girki da rabon abincin buda baki a matakai daban-daban na kananan hukumomi.