✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ramadan: Gwamnatin Kano za ta kashe N550m wajen ciyarwar azumi

Za a ciyar da abincin ne a cibiyoyi 140 da ke cikin kwaryar birnin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da kwamitin da zai kula da ciyar da marasa karfi a fadin Jihar yayin watan azumin Ramadan.

Da yake kaddamar da kwamitin ranar Lahadi, Mukaddashin Gwamnan Jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, ya hori mambobinsa da su kwatanta gaskiya yayin aikin nasu.

Ya kuma jaddada muhimmancin ciyarwa a addinin Musulunci, inda ya shawarci sauran mutane da su shiga a dama da su a cikin aikin ladan.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautun Gargajiya na Jihar, Lawan Hamisu Danhassan ya fitar ranar Lahadi.

Sanarwar ta ambato Kwamishinan ma’aikatar, Murtala Sule Garo na cewa an ware Naira miliyan 550 don aikin ciyarwar a cibiyoyi 140 da aka ware a Kananan Hukumomi takwas na cikin birnin Kano.

Ya ce kayan da za a dafa sun hada da shinkafa da wake da fulawa da gero da manja da kuma man gyada.

Kwamishinan ya kuma ce gwamnati za ta ci gaba da fadi-tashi wajen ganin ta tallafa wa marasa karfi a Jihar.

%d bloggers like this: