✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ramadan: Ba ma bin ganin watan Saudiyya —Sarkin Musulmi

Abin da ya sa Najeriya ba ta amfani da ganin watan Saudiyya

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa Najeriya ba ta bin ganin watan kasar Saudiyya wurin daukar Azumin Ramadan.

Sarkin Musulumi ya ce a sha’anin ganin watan azumi, ana aiki ne da ganin watan al’ummar Musulmin Nijeriya da aka tabbatar da gaskiyar ganin watan nasu.

“Ba mu bin Saudiya a ganin watan Ramadan, muna amfani ne da ganin watan al’ummar Musulmi a wurare daban-daban,” a cewarsa.

Ya ce Najeriya ba ta la’akari da ganin watan Saudiya ne saboda Saudiyya na amfani da kalanda a sauran watannin ba ba na Azumi da Hajji ba, shi ya sa Najeriya ba ta dogaro da ganin na Saudiyya.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya ce ya yi maganar ne kusan wata biyu kafin Azumin Ramadan don kar a samu rudani, ganin yadda aka fara ce-ce-ku-ce kan ganin wannan watan da ya soma.

Ya yi bayanin ne a wurin bikin kaddamar da littafan Musulunci uku da Dakta Jabir Sani Maihula ya wallafa da aka yi Makarantar Haddar Al-Kur’ani ta Maccido da ke Sakkwato.

Ya bukaci malamai su tashi tsaye wajen fadakar da mutane abin da ya wajaba a gare su da kuma sha’anin duban wata.

“Mutane ba su san yadda ake duba wata ba; in wata ya fito sai ka ji suna fadin ya girma.

“Kai ina ruwanka in matsala ce tana wurinmu, ba mu yanke hukunci kara zube,” inji shi.

Ya yi kira da a taimaki juna kar a rika fada kan rashin gaskiya, a rika ba juna hakuri da fadakarwa kan addinin Musulunci da tsare-tsarensa.

Game da cutar COVID-19 kuma ya ce, “Gaskiya ce, kar mu ce babu ita, mu yarda mu sa takunkumi dole ne na dan lokaci,” a cewar Sarkin Musulmi.

Sai dai bai ce uffan kan hatsaniyar da ta kaure tsakanin kungiyoyin Musulunci a Sakkwato da Rabaran Mathew Hassan Kuka a satin da ya gabata ba, har suka ba shi wa’adin barin Sakkwato.