✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: An kaddamar da keken rabon ruwan Zam-Zam a masallatan Harami

Za a iya bi cikin sahu da kekunan don saukaka wa masu ibada shan ruwan Zam-zam.

Babban Limamin Masallacin Harami Sheikh Abdurrahman Al-Sudais, ya kaddamar da wasu sabbin kekunan jigilar rarraba ruwan ZamZam a masallatan domin saukaka wa masu ibada a yayin da watan Ramalana ya karato.

Sheikh Sudais wanda shi ne Shugaban lura da al’amura a Masallatan Harami ya kaddamar da kekunan ne tare da mataimakinsa, Dokta Saad bin Muhammad Al Muhaimid a ranar Lahadi.

Kekunan shayar da ruwan zamzam din da aka kera da karfe mai jure tsatsa, suna dauke da dundukai biyu masu daukar lita 80 na ruwa a lokaci guda.

Ruwan Zam-Zam mai sanyi yana tsiyaya a daga bakin famfon
Sheikh Sudais yana gwada yadda ruwan zai rika tsiyaya
Sheikh Sudais yayin kaddamar da kekunan

An kera kekuna ne ta yadda za su rika bayar da ruwan sanyi da kuma madaidaici tare da sanyawata na’urar tsaftace ruwan da kawunan famfon a matsayin wani mataki na hana kwayoyin cututtuka zama a jikinsu domin kare lafiyar masu ziyarar masallatan.

In yi injinan ne ta yadda za su yi saukin turawa a tsakanin sahun masallata wanda ya yi daidai da duk wasu matakan dakile yaduwar cututtuka da mahukuntan lafiya suka shar’anta.