✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: A soma laluben wata ranar Juma’a —Sarkin Musulmi

A soma duba jinjirin wata na Ramadana daga ranar Juma'a.

Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya ta umarci al’ummar Musulmi da su soma duban watan Ramadan daga ranar Juma’a 29 ga watan Sha’aban shekara ta 1443 Bayan Hijira wanda ya yi daidai da 1 ga Afrilun 2021. 

Majalisar da ke karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ta bayyana hakan ne cikin wani sako da ta fitar mai dauke da sa hannun Daraktan Gudanarwa, Zubairu Haruna Usman-Ugwu.

Sanarwar ta nemi duk wanda ya ga jinjirin watan da ya kai labarin ga basaraken da ke kusa da shi domin sanar da Majalisar Sarkin Musulmi ko Kwamitin Ganin Watan na Kasa da masarauta.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa muddin ba a samu ganin jinjirin watan ba a gobe Juma’a, to Sarkin Musulmi zai ayyana ranar Lahadi, 3 ga watan Afrilu a matsayin 1 ga watan Ramadana kamar yadda addinin Islama ya tanada.

Kazalika, cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Sakataren Fadar Sarkin Musulmi, Yahaya Muhammad Boyi da ke zaman Sarkin Malaman Sakkwato, ta ce bayar da lambobin waya da duk wanda ya samu ganin watan ko labarin zai iya magana da kwamitin ganin wata kai tsaye.

Lambobin su ne kamar haka: 08037157100, 070674116900,  08066303077, 08036149757, 08035965322 da 08035945903.