Majalisar Wakilai ta kara sati takwas a kan wa’adin da Hukumar Sadarwar ta Najeriya (NCC) ta sanya na rufe layukan waya da masu su ba su yi rajista da lambar shaidar dan kasarsu (NIN) ba.
A ranar Talata NCC ta umarci kamfanonin sadarwa su sanya lambar NIN din masu amfani da wayoyi a cikin mako biyu wanda za a rufe ranar 30 ga Dimsamb, 2020 wanda daga nan za a rufe layuka marasa NIN.
- Abin da ya sa na tube Sanusi daga Sarautar Kano —Ganduje
- Sakon Shekau: Sojoji da Fadar Shugaban Kasa sun yi gum
Sai dai Majalisar Wakilai ce a kara lokacin bayan Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu ya bukaci a kara wa’adin ne zuwa mako hudu, bisa hujjar cewa umarnin ya zo a kurarren lokaci kuma ba a wayar wa jama’a kai ba.
“Yunkurin aiwatar da dokar a lokacin da jama’a ke shirin tafiya hutun karshen shekara zai kawo turereniya da yiwuar samun rauni ko mutuwa a wuraren yin rajista.
“Idan aka bar NCC ta aiwatar da shi to miliyoyin Najeriya da za a rufe wa layi a lokacin bukukuwan karshen shekara za su shiga mawuyacin hali kuma yana iya jefa kasar cikin karin matsaloli.
“Idan ba a hana ba to mutane za su shiga cikin zullumi wanda ke iya kaiwa ga cutar da masu rauni”, inji Elumelu.
Bayan muhawara, Majalisar ta amince a kara lokacin zuwa mako 10 don jama’a su gabatar da lambar NIN din su.
Ta kuma kafa kwamiti da sai da ido domin tabbatar da bin umarnin.
Sabon umarnin na NCC dori ne a wanda ta bayar a baya na rufe sayarwa da kuma rajistan sabbin layukan waya a Najeriya.