✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahoton kwamitin majalisa: Kada ya zama gyaran gangar Azbinawa

A makon jiya ne Kwamitin Majalisar Dattawa kan gyaran kundin tsarin mulki ya mika rahotansa a zauren majalisa. Rahoton na kunshe da batutun da tuni…

A makon jiya ne Kwamitin Majalisar Dattawa kan gyaran kundin tsarin mulki ya mika rahotansa a zauren majalisa. Rahoton na kunshe da batutun da tuni suka haifar da cece-kuce a kasa, kuma ana tsammanin za a ci gaba da tattauna batutuwan bayan majalisa ta dawo daga hutun tsakiyar shekara da ta tafi. Shugaban kwamitin, Sanata Ike Ekweremadu a lokacin da yake jawabi kan rahoton ya ce, kwamitin ya bukaci a samar da zangon mulki daya na tsawon shekara shida ga shugaban kasa da gwamna, a nada magajin garin Abuja, a rushe hukumomin zaben jihohi, a daina asusu hadin-gwiwa tsakanin jihohi da kananan hukumomi don kananan hukumomi su rika cin gashin kansu.
Haka kuma kwamitin ya ki amincewa a kirkiro sababbin jihohi, inda ya ce duk masu neman a kirkiro sababbin jihohin ba su cika ka’idar da dokar kundin tsarin mulki sashi 8 (1) da aka yi masa gyara a shekarar 1999 ya tanadar ba. Duk da haka za a iya zama don sake duba wadannan batutuwa, wanda a yanzu ma batutuwan sun haifar da cece-kuce.
Tun lokacin da aka fara takaddamar gyara kundin tsarin mulki, majalisar Dattawa ce ta rika kamfen a kirkiro sababbin jihohi, duk da cewa wadansu sun ce kirkiro jihohin ba za su sanya kwalliya ta biya kudin sabulu ba.
Tabbas kirkiro sababbin jihohi ba dabara ba ce, musamman idan aka yi tunani ko a yanzu ma ana kashe makudan kudade a kan ’yan majalisa da kuma jami’an gwamnati, wanda kamata ya yi a nemi hanyar da za a rage kudaden da ake kashewa a kansu. Ko a yanzu ma jihohi da dama sun dogara da kason da suke samu daga asusun gwamnatin tarayya duk wata don gudanar da ayyukansu.
A cikin batutuwan da kwamitin ya bukaci a tabbatar babu abu mafi mahimmanci kamar a ba kananan hukumomi cin gashin kansu. Asusun hadin gwiwa ba shiri ne mai kyau ba, kowa ya ga yadda gwamnatin jiha ke uwa da makarbiya a kan asusun ba tare da jihohin sun amfana daga shirin kamar yadda ya kamata ba.
Hukumomin zabe na jihohi ba su taka muhimmiyar rawa wurin aiwatar da ayyukansu yadda suka kamata wurin taimaka wa dimokuradiyya ta tsaya da gindinta a matakin jihohi ba, don haka ko da za a rushe su ba za su sanya a shiga wani halin damuwa ba, amma kuma ta wani bangaren dabarar rashin dabara ce a dora nauyin gudanar da zaben kananan hukumomi a kan hukumar zabe ta kasa (INEC), idan aka yi dubi da yadda hukumar take fama wajen gudanar da zabe mai inganci da jama’a za su amince da shi. Kamar yadda ake zargin gwamnonin jihohi na juya hukumomin zaben jihohinsu don cin zabe, haka za a yi zargin jam’iyya mai mulki a kasa za ta iya amfani da hukumar zabe ta kasa don ta ci zaben shugabannin kananan hukumomi da kuma kansiloli. Don haka shawara a nan ita ce, a samar da matan da za su takaita ikon gwamnoni a kan hukumomin zaben jihohi maimakon a rushe su.  
Ga batun amincewa da zangon mulki karo daya na tsawon shekara shida bai ma taso ba, wannan cin dunduniya ne ga dimokuradiyya. hakan zai zama kamar takin zamani ne wurin habaka cin hanci da rashawa.
Don haka ya kamata majalisa ta yi la’akari da ra’ayoyin jama’a lokacin da ta gudanar da sauraren koken jama’a, ba wai abin da kwamitinta ya bukaci a yi ba.
Bugu da kari, muna fata majalisa za ta tsaya kai da fata wurin gyara batutuwan da za su karfafa dimokuradiyya da kuma wadanda za su dace da ra’ayoyin al’umma, idan ba haka ba kuwa sai a ce gyaran kundin tsarin mulki zai zama gyaran gangar Azbinawa.