✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rahama Sadau ta yi nadamar batancin da hotunanta suka jawo

Rahama Sadau ta yi nadamar mummunan abin da hotunanta da ta yada suka haifar

Bayan ce-ce-ku-ce da tir da jaruman masana’antar Kannywood suka yi wa jaruma Rahama Sadau, da kuma wanda mutane suka yi bayan ta saki wasu hotuna da suke nuna jikinta, jarumar ta fito a wani bidiyo tana kuka, inda ta nemi afuwar mutane da abokan aikinta baki daya.

A cewarta, “Ni Musulma ce. Ban saka wadannan hutuna domin abin da ya faru, ya faru ba.

“Ba zan taba yin abin da zai taba Musulunci ko Annabi Muhammad S.A.W. ba

“Kuma dama muna wani irin lokaci ne yanzu wanda ake neman wata gaba da a ci mutuncin Musulunci; Sai kuma kaddarar ta fada a kan hotona.

“Ni ba mahaukaciya ba ce, ba ni da dalilin amincewa da abin wannan mutumin ya rubuta a kasan hotona; Amma dai kaddara ta riga fata.

“Duk abin da ya faru, ya faru ne a dalilina. Ina mai ba daukacin al’umma hakuri. Don Allah a yi hakuri.”

Aminiya ta ruwaito yadda jaruman Kannywood suka yi ca a kan jarumar, inda wasu har da tsinuwa suka yi.

 

View this post on Instagram

 

Na yi wannan video din ne cikin nadama da takaici. Ina kuma mai ba da hakuri bisa abin da ya faru ga dukkanni Hausawa, abokan aikina da musulmai baki daya bisa wannan hoto nawa da ya jawo wannan cece-ku-ce. Wannan ba dabi’a ta ba ce a matsayina ta musulma. Ni masoyiyar Manzon Allah (SAW) ce, kuma Ina yaqi da duk wani wanda ya taba shi ko ya taba addinina. Kaddara ce ta kawo kawo har wani yayi batanci akansa Akan hotona. BANA TARE DASHI, Allah kuma ya la’ance shi Akan wannan batanci da husuma daya tayar a Lokacin da duniya ke cikin wani Hali . Haka ba zai kara faruwa a kai na ba insha Allah. Na gode Allah ya kare mana imanin mu da addinin mu. Rahama Sadau❤️

A post shared by R A H A M A S A D A U (@rahamasadau) on