✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ragwaye ne kawai ke kayyade iyali – Shugaban Tanzaniya

Shugaban Tanzaniya, John Magafuli ya ce ragwaye ne suke kayyade iyali, inda ya yi kira ga ma’aurata a kasarsa su ci gaba da haihuwar ’ya’ya.…

Shugaban Tanzaniya, John Magafuli ya ce ragwaye ne suke kayyade iyali, inda ya yi kira ga ma’aurata a kasarsa su ci gaba da haihuwar ’ya’ya.

Kafar labarai ta kasar mai suna Citizen, ta rawaito Mista Magafuli yana cewa kayyade iyali ne ya janyo raguwar yawan al’umma a Nahiyar Turai da kuma matsalar karancin ma’aikata.

Shugaban kamar yadda Citizine ta ruwaito, yana magana a kauyen Mearu da ke gabashin Tanzaniya, yayin da yake jawabi a gaban wakilin Hukumar Kula da Yawan Jama’a ta Majalisar dinkin Duniya a Tanzaniya, Jackueline Mahon da kuma Ministar Lafiya, Ummy Mwalimu.

A yayin jawabin wanda mafi yawan mahalarta taron manoma ne, Mista Magafuli ya ce, “Masu tsarin iyali malalata ne. Suna tsoron cewa ba za su iya ciyar da ’ya’yansu ba. Ba sa son yin aiki tukuru domin ciyar da iyalansu. Don haka ne suke kayyade iyali, sai ka ga sun buge da haihuwar da daya ko biyu kawai.”

Ya kara da cewa, “Na je Turai da wasu wurare, na ga illar tsarin iyali. A wasu kasashen ma fama suke yi da karancin haihuwa. Ba su da ma’aikata.”

To sai dai wani dan Majalisar  Dokokin kasar, Cecil Mewambe ya soki kalaman na Shugaba Magafuli, inda a zauren majalisar ya bayyana cewa tsarin inshorar lafiyar kasar zai iya daukar nauyin mutum hudu ne kawai daga kowane iyali.