✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ragowar fasinjojin jirgin kasan da ke hannun ‘yan ta’adda na cikin tsaka mai wuya – Tukur Mamu

Ya ce labarin cewa an saki dukkansu ba gaskiya ba ne

Dan jaridar nan mai shiga tsakanin ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjojin Abuja zuwa Kaduna, Tukur Mamu, ya ce har yanzu akwai ragowar mutane a wajensu kuma suna cikin tsaka mai wuya.

Ya ce sabanin yaddda ake yadawa a wasu jaridu da kuma shafukan sada zumun na intanet, har yanzu akwai ragowar mutanen a hannunsu.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Malam Mamu ya ce har yanzu akwai sauran fasinjoji 27 dake hannun ‘yan ta’addan wadanda suka shafi wata biyar ke nan a cikin daji.

Kazalika ya ce ya janye daga shiga tsakani wajen tattuanawa da ‘yan ta’addan wanda ta kai ga sakin wasu da aka yi garkuwa da su a baya, ya kuma daina shiga lamarin.

Sai dai ya ce matsin lamba daga ‘yan uwa da dangin wadanda ke hannun ‘yan ta’addan da kuma ‘yan jarida na son jin gaskiyar labarin ya sa ya fitar da sanarwar tare don tabbatar wa duniya cewa labarin sakinsu karya ne.

Tukur Mamu ya kuma ce yana fatan ganin Gwamnatin Tarayya ta dada matsa kaimi wajen ganin an sako sauran mutanen saboda yanayin da suke ciki a daji ya sa yawancinsu na fama da rashin lafiya.

“Ina mi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya yi duk mai yiwuwa ya ga an kubuto da wadanda suke tsare a hanunsu cikin gaggawa saboda halin da suke cikin na kila-wa-kala [dangane da lafiyarsu].”