✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rage albashi a Kano ya tayar da kura

Ma'aikata sun ce abin da aka biya su bai kai na lokacin mafi karancin albashin N18,000 ba

Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano sun ce sun girgiza da zaftarar da Gwamnatin Jihar ta yi wa albashinsu na watannin Nuwamba da Dismaban 2020.

Ma’aikatan sun ce abin da ya rage musu bayan yankan da aka yi wa albashin nasu bai kai tsohon mafi karancin albashi na N18,000 ba.

Sai dai jami’an Gwamnatin Jihar Kano sun musanta cewa mayar da albashin zuwa tsohon mafi karancin albashi aka yi, inda suka ce wani koso na albashin ma’aikatan aka cira saboda matsalolin da Najeriya ke ciki bayan bullar annobar COVID-19.

A shekarar 2020 ne Gwamnatin Tarayya ta kara mafi karancin albashin ma’aikata zuwa N30,000, matakin da wasu jihohi suka runguma ciki har da Jihar Kano tare da yi wa ma’aikatansu kari gwargwadon matakinsu na aiki.

Ma’aikatan Jihar Kano sun shaida wa Aminiya cewa babu adalci a zaftarar albashin nasu, domin a watannin Nuwamba da Disamba da aka yi gwamantin ta fitar da biliyan N2.3 don gudanar da zaben kananan hukumomi na ranar 16 ga watan Janairu.

Yawancin ma’aikatan sun diga ayar tambaya game da abin da gwamnatin ke yi da kudaden da take samu daga Gwamnatin Tarayya, haraji, tallafin kasashen waje da sauran sauran kudaden shiganta.

Aminiya ta gano cewa Jihar Kano ba ita ce kadai ta taba albashin ma’aikatanta ba a baya-bayan nan.

Ana iya tunawa Gwamnatin Jihar Neja ta ce ba za ta iya biyan kashi 100% na alabshin ma’aikata ba; Gombe kuma ta dakatar da biya sabon mafi karancin albashin N30,000 tun a watan Maris na 2020.

Gwamnatocin jihohin biyu sun danganta matakin da suka dauka da illar da suka ce annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arzikin Najeriya.

‘Ba za mu iya ba’

Hadimin Gwamna Abdullahi Ganduje kan Shafukan Sada Zumuta, Salihu Tanko Yakasai, ya sanar a ranar Laraba cewa “gwamnatin jihar ta koma biyan tsohon mafi karancin albashi saboda durkushewar tattalin arziki.

“Abin da gwamnatinmu ke samu yanzu ya ragu kuma ba za mu iya biyan mafi karancin albashin N30,000 ba.”

Yunkurinmu na samun bayani daga Shugabar Ma’aikatan Jihar Kano, Binta Ahmed, bai yi nasara ba.

Mun kira wayarta muka kuma tura mata rubutaccen sakon da alama ta nuna ya shiga wayarta, amma ba ta waiwaye mu ba har muka kammala hada wanann rahoto.

Wakilinmu ya je ofishinta a Sakatariyar Jihar ta Audu Bako, inda aka shaida masa cewa ba ta shiga ofis ba a gaba daya ranar (Laraba).

Sai dai Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Muhammad Garba, ya ce ba komawa biyan tsohon mafi karancin albashi na N18,00 aka yi ba, ragi ne dai aka samu saboda yanayin da tatttalin arzikin kasa ya shiga.

Ragin da aka yi dai ya shafi ma’aikata 55,505 a hukumomi da ma’aikatun da kuma manyan makarantun Gwamnatin Jihar Kano tun daga ranar 31 ga watan Disamba, 2020.

Sai dai bai shafi ma’aikatan Jami’ar Yusuf Maitama Sule da kuma Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KSTU Wudil) ba.

Ragin ya kuma sahifa daukacin masu rike da mukaman siyasa a Gwamnatin Ganduje.

‘Kasa da N18, 000 aka koma’

Aminiya ta zanta da ma’aikatan gwamnatin jihar wadanda suka bukaci mu sakaya sunayensu.

Wani ma’aikaci a Hukumar Kula da Malamai (TSB) ya ce an zaftari albashinsu a watannin Nuwamba da Disamban 2020 ba tare da wani bayani ba.

Ya ce duk da cewa gwamnatin ta koma biyan tsohon mafi karancin albashi na N18,000, amma abin da aka cira a albashinsa na Disamba ya haura karin da aka yi masa bayan kara mafi karancin albashin zuwa N30,000.

Saboda haka abin da ya rage masa bai kai albashin da yake karba a lokacin mafi karancin albashi yake N18,000 ba kuma ba shi kadai hakan ta faru da shi ba.

Wani ma’aikaci a wata ma’aikatar jihar ya ce zarar da aka yi wa albashinsu kwatsam a Disamba ya sanyaya wa ma’aikata gwiwa.

Sai dai ya ce bai ga laifin gwamnatin ba sai laifin kungiyoyin kwadago da suka ja bakinsu suka yi gum.

“An yi ta zarar albashinmu a tsawon lokacin kullen COVID-19 kuma kowa ya fahimta; amma wannan zaftarar ta yanzu, laifin kungiyar kwadago ne da ta ki magana a kai; ba mu san da wa za mu dogara ba,” inji ma’aikacin.

Ita ma wata ma’aikaciyar gwamnatin jihar da muka yi hira da ita ta ce abin da ya same su da cewa ‘Gatarin Ganduje’ ne ya fada a kansu.

Ta ce a yanzu babu ma’aikacin jihar da ya san hakikan abin da za a biya shi a matsayin albashi a karshen wata.

Haramtaccen mataki

Mun zanta da Shugaban Kungiyar Kwadaga ta Najeriya (NLC) Reshen Jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado wanda ya ce Kwamitin Tattaunawar Hadin Gwiwa (JNC) ne ke da alhakin tattaunawa a matakin jihar ba NLC ba —“amma NLC kawai tana zama shaida ce”.

Ya ce “Ba mu samu wata sanarwa a hukumace daga Gwamantin ba cewa za ta koma biyan tsohon albashi kamar yadda kafafen yada labarai ke ruwaitowa. Saboda haka za mu ci gaba da zama a kan yarjejeniyar da aka sanay wa hannu a watan Disamban 2019 na mafi karancin albashi na N30,000.”

Mun kuma gana da Shugaban JNC  na NLC a Jihar Kano, Kwamared Hashim Saleh, wanda ya ce ba da yawun ’yan kwadagao aka dauki matakin ba, sannan ko da ta tuntubi gwamnatin jihar ta dakatar da cirar kudin a watan Disamba, gwamnatin ba ta yarda ba.

“A watan Nuwamban 2020 suka yi gaban kansu suka rage kudaden sabanin yarjejeniyar da aka rattaba wa hannu bisa tanade-tanaden Yarjejeniyar Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO). Sun yi abin da suka yi ba tare da bin matakan da suka dace ba,” inji shi.

Ya ce dokar ILO ta tanadi cewa idan gwamnati na da matsalar kudaden shiga, to sai ta kira zama wakilan ma’aikata “su zauna sun tuba bayanan kudaden da gwamnati ke kashewa” domin wakilan ma’aikatan su gani su kuma fahimci hakikanin halin da ake ciki.”

Ya ce, “Bayan binciken da muka gudanar, mun rubuta wa gwamnatin jihar wasika cewa ta dakatar da cirar kudin sannan ta dawo wa ma’aikata kudaden da aka cira. Mun tura takardar ta hannun Shugaban Ma’aikatan Gwamna muka kuma tura kwafin wasikar ga daukacin masu ruwa da tsaki.

“Gwamnatin ta gayyace mu a Disamba tare da Shugabannin NLC, TUC ds sauran masu ruwa da tsaki cikin har da wadanda ba sa cikin JNC da TUC sun halarta.

“Gwamnatin ta shaida mana cewa tana fama da matsalar kudi, amma muka gaya mata cewa babu wannan maganar a lokacin.

“A lokacin da muka yi tattauanwar, kudaden da Gwamnatin Tarayya ta raba bai kai biliyan N600, amma na watan Nuwamba ya haura biliyan N600, don haka ba mu yarda cewa babu kudi ba”.