kasar Amurka ko ‘Amari-kowa,’ a cewar masu koyon watsatsake da buda wagagen litattafai na wannan farfajiya, kasar na ban ta’ajibi, ganin yadda take da manyan masana, wadanda suka ci farrfesun ilimi a fannin tsimi da tanadi, irin su Rabon Sulalla . A kasar Uban-Mama, Jikan Kenyawa jagoran Amurka, akwai hamshakan attajirai irin su Wararren Bappan Amurka da Bilyan Gata, wadanda kasar ke ci ta gyatse a cikin lalitarsu. Mu kuwa Haurobiyawa, babu abin da su Audu-Tela da dangatan kasuwa ke tsinana mana illa kashe mu-raba da jami’an hukuma. Su kuwa masana sun zama marasa sana’a, domin wasunsu neman sa’ar wasoso suke yi don neman yin ‘su’ a lalitar kasa.
Babban abin ta;ajibi shi ne kasancewar Rabon Sulalla a jerin Jami’an Asusun ilimi na kasar Amurka, ya ci lambar yabo ta Nobel, bisa la’akari da kwazonsa wajebn zakulo manger fasko dabarun sarrafa dukiya, inda ya nuna wa al’ummar duniya cewa ‘ba ana nufin dabarun sarrafa su kasance na tara damin dukiya ba, a’a, wata hanya ce ta biyan bukatunmu al’umma,’ wato a samu Hauron sayen kayan dumdume kururu da tufafi da matsugunni tsugunnawa.
A Afirka ya ya muka dauki harkar sarrafa Hauro? Madubin dubawarmu dai ita ce Giwar Ifrikiyya, wato Haurobiya. Batu na-ingarman karfe, Haurobiya ta zama gidan kwashi kwaraf, inda masu mulki ke aiwatar da tsare-tsaren kassara al’umma. Sun haifar da wawakeken gibi a tsakanin talakawa da masu mulki; Gwamnati ta cefanar da dukiyar al’umma, inda ta yi wa ’yan lelenta suka gwangwaje da gwanjo kamfanonin Haurobiya.
Manyan Haurobiya kullum neman sila wadda ta fi salsala da salala, ta yadda idan sun ga galala, sai su dinka galila. Idan mahukunta suka sulale da sulalla, talakawa sai dai su ji a salansa. Duk da cewa mummunan yanayin da Haurobiyawa suka samu kansu a ciki, bai rasa nasaba da mulkin-mulaka’u irin na Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, wajibi ne mu dora babban laifi a kan masana tsimi da ta’adi irin su In-gwangwaje-in-wala da Masanin Sisi-da-sisi, domin yau sun bar Lado da Okonko da Lasisi ba su da ko asi.
To ga kalubale ga masanan tsimi da ta’adi da suka kware wajen jefa Haurobiyawa a cikin tsamiyar tsiya, lallai su yi koyi da Wararren Bappan Amurka da Farfesa RAbon Sulalla, wadanda suka himmatu ka’in da na’in don kyautata rayuwar al’umma. Ba ni da wani haufi, masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a farfajiyar Dodorido da ke Amintatar jarida ta kasar Haurobiya za su ari tagiyar Malam Tunau, don lalaubo darasinmu kan yadda Wararren Bappan Amurkawa ya jajirce wajen ganin a kara tsuga wa masu tarin dukiya dimbin haraji, ta yadda za su rage wa talakawa nauyi. Me yasa mu a Haurobiya kullum sai kara jibga wa al’umma nauyaye-nauyaye ake ta yi?
Ga shi dai za su hana cinikin na kwadi a cikin leda, inda za su bullo da nasu na roba mai hoton agwagwa. Sun hana zabari da baburido, ba su yi wa matasa masu jini a jika tanadin komai ba. Kodayake wasu ’yan lele an dora a kan layin Yawon wuni-wuni. Wasu kuwa an gurbata tarbiyarsu. Domin a jerin masu jan ragamar kasar nan, akwai Akuyar-maman-dauduk, wanda ya taba cewa duk macen da ke sha’awar karo-karon-wawanci, sai kawai a bat lasisi, don ta samu hanyar tara taro da sisi.
Lokaci ya yi da za a daina kassara talakawa, a daina yi musu sasarin talalar talauci, ta hanyar raba musu tallafin koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a cikin yaren Hau-hau wajen hawan sa, ba tare da sa-in-sa ba. A kyautata harkokin kula da uwar jiki, a daina yi mana na jaki a farfajiyar bokan Turai. Kuna gani dai shi kansa Uban-Mama kokarin Tarawa talakawansa hanyar kula da uwar jikinsu ta janyo masa kiki-kaka a gwamnatinsa. Mu kuwa kwakyariyar mahukunta ta janyo wa Jatau Mai-sa-in-sa ya sanya kafar wando da Jami’an Asusun Ilimi da ke kwadago a jam’in jama’ar jami’o’in Haurobiya.
Masanan tsimi da tanadi, sai ku lalubo wa Haurobiyawa dabarun rabon dukiyar kasa cikin adala, ko kuma rage badala, idan kuwa kun nuna gazawa, to zan yi tsallen badake, in bugi kirji in ce nin Farfesa Rabon Sulalla, zan kuma raba sulalla kowa ya samu. Babu sauran salalar sulallewa da sulalla, balanta mu ji a salansa. Dabarun sarrafa dukiyar al’umma ba yana nufin hamdama da babakere ba, a’a, abin da ake nufi shi ne ku raba wa ’yan kwadago Albukata, sabanin Allah Ba ni in biya ba shi da kuke dan difara musu. Wannan mummunan tsari naku shi ya share wa jaba da gafiya da kusu wuri suke ta wadaka a kasar Haurobiya. A daidai lokacin da muke taya Farfesa Rabon Sulalla murnar lashe lambar yabo ta Nobel, muna kuma yi wa masu shirya wa Haurobiyawa kunbiya-kunbiyar makirci albishiri da cewa ‘kashinku ya bushe!’
…Barka da Salla
Haurobiyawa kun ga mu kadai ke raba sulalla. Don haka kowa ya dawo makaranta. Don za mu rika raba ca’ammas da zarar mun ziyarci birnin Tagadas.