Ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Chris Ngige, ya bukaci masu da’awar cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba ya adalci wajen raba mukaman gwamnati da su rufe bakinsu.
Ya ce ire-iren wadannan mutanen ba su ma san yadda ake tafiyar da gwamnati ba sam.
- Muna bukatar addu’o’in samun galaba kan Boko Haram — Janar Abimbola
- Masu gurasa sun fara yajin aiki a Kano
Ngige ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Abuja yayin wani taron gaggawa da kungiyar ’yan kabilar Ibo mazauna jihohin Arewa 19 da Abuja suka shirya.
An dai shirya taron ne domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan yawan kashe-kashe tare da lalata kadarorin gwamnati da ke faruwa a Jihohin Kudu maso Gabas.
Ministan ya jaddada cewa su kansu ’yan kabilar Ibon an nada su a manyan mukaman gwamnatin.
Ya ce, “Mutane na cewa wai ba a ba mu mukaman irin su Sufeta Janar na ’Yan Sanda da Babban Hafsan Sojin Kasa da Sakataren Gwamnatin Tarayya. Ai wadannan mukaman mun rike su a can baya.
“Mun samu Sufeta Janar har guda biyu, Ogbonna Onovo da Mike Okiro.
“Mun taba yin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata Pius Anyim. Mun yi Shugabannin Majalisar Dattawa guda hudu.
“Sau biyu muna samun Mataimakan Shugaban Majalisar Dattawa da na Kakakin Majalisar Wakilai, Ike Ekweremadu da Emeka Ihedioha.
“Sune da wuka da nama a kasafin kudin tarayya na shekara takwas daga 2007 zuwa 2015.
“Idan kana maganar raba mukamai ne, ya danganta da yadda ka fahimci abin. Ba na zargin su.
“Fahimta da yadda lamarin abin yake a zahiri duka abu guda ne. galibinsu ba su fahimci yadda ake tafiyar da gwamnati ba.
“Akasarinsu ba su san cewa a matsayina na mamba a Majalisar Zartarwar Tarayya zan iya yin wani katabus kan abin da jiha ko yankina ko kuma duk wani wuri inda muke tunanin ya kamata a kai ko gina wani abu ba.
“A wajena, ire-iren wadannan mutane masu wannan tunanin jahilai ne,” inji Ngige.
Ya ce Shugaba Buhari ya nuna wa ’yan kabilar Ibo kauna a shekara shida da ya shafe yana mulkin Najeriya duba yadda ya ce yankin Kudu masu Gabas din ya samu daidai gwargadon abin da ya kamata ya samu ta fuskar ababen more rayuwa.