Gwamnan Jihar Bauchi kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP, Bala Mohammed, ya raba kafa inda ya sayi fom din takarar Gwamna a boye, bayan ya riga ya sayi na Shugaban Kasa.
Duk da cewa an tantance shi gabanin zaban fid-da gwani wanda za a yi a ranar biyu ga watan Mayu na 2022, kamar yadda jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito.
- PDP: ‘Masu neman takarar Shugaban Kasa 2 sun yi asarar kudin fom dinsu’
- Zaben 2023: Za a fara tantance ’yan takarar PDP
Bayan neman tikitin takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar PDP, jaridar ta ruwaito cewa Gwamnan na Bauchi ya sayi fim din.
Gwamnan dai zai kammala wa’adin mulkinsa na farko a shekara ta 2023. Wanda hakan zai iya ba shi damar sake tsayawa takara a karo na biyu.
Tun bayan bayyana kudirinsa na tsayawa takarar Shugaban Kasa dai ne aka ta kai kawo akan wanda zai maye gurbinsa a kujerar Gwamnan a 2023.
Wannan cece-kuce ya sa ake tunanin cewa Sakataren Gwamnatin Jihar, Ibrahim Kashim, ne zai maye gurbinsa a matsayin Gwamnan.
Ikirarin ya bayyana cewar Kashim din ya ajiye mukaminsa a boye domin tsayawa takarar Gwamnan.
Rahoton ya kuma ce idan sakataren ya samu lashe zaben fitar da gwanin da jam’iyyar za ta yi, idan shi kuma Gwamnan bai samu tikitin takarar Shugaban Kasa ba, to zai maye gurbin Kashim a matsayin dan takarar Gwamnan.
Sai dai kakakin gwamna Bala Muhammad ya musanta tare da cewa wannan wani labari ne mara tushe.
“Ni ba na magana akan irin wadannan labarun da ba su da tushe, kawai abin da na sani shi ne an tantance shi domin shiga cikin jerin masu neman takarar shugaban kasa,” inji shi.
Sai dai majiyarmu ta bayyana mana cewa Bala Muhammed ya sayi fom din takarar Gwamna domin akwai yuwuwar ya janye daga cikin masu neman tsayawa takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar.