Masana harkar siyasa da sauran ’yan Najeriya sun bayyana wasu muhimman abubuwa 10 da za su inganta harkar zabe a Najeriya daga cikin da sabuwar dokar zaben da Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.
Tun bayan sanya hannu kan dokar manyan ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki suka shiga bayyana ra’ayoyinsu dangane da irin rawar da sabuwar dokar za ta taka wajen inganta harkar zabe a kasar nan.
- Gwamnatin Kano ta sallami wasu ma’aikata kan zargin cefanar da filaye
- ASUU: An tashi baran-baran a tattaunawar Ministan Ilimi da shugabannin dalibai
Kadan daga cikin daga abubuwan da suke cewa kan dokar zaben ta 2022 wadda Buhari ya sanya wa hannu a makon da ya gabata.
1. Fitar da jadawalin zabe
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, cewa ya yi, “Tunda komai ya kankama game da zaben 2023 bayan Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar zaben da aka yi wa gyaran fuska.
“Saura kuma hukumar zabe ta fitar da jadawalin yadda jam’iyyu za su bi don ba wa ’yan Najeriya damar zaben shugabanninsu a 2023.”
Tuni dai INEC ta fitar da jadawalin babban zaben da za a gudanar nan da wata 12 masu zuwa.
2. Fasahar zamani zai kara wa zabe inganci
Auwal Musa Rafsanjani, mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum kuma babban darakta a kungiyar CISLAC, wato kungiyar da ke sanya ido a kan ayyukan majalisu da yaki da cin hanci.
Ya ce, “A cikin manya-manyan gyaran da aka yi a dokar zabe shi ne tura sakamakon zabe ta fasahar zamani ba kamar da ba, idan aka gama zabe a nan kowa zai san me aka ci a nan, kowa zai san sakamakon zabe daga hukumar zabe ta hanyar fasahar zamani.
“Sannan an samu gyara kan fitar da sakamakon zabe, idan an tilasta jami’an hukumar zabe, an ba su damar sake duba sakamakon, an ba wa hukumar zabe damar bin diddigin abin da aka yi.”
3. Kayyade amfani da kudi
Shi kuwa Kwamared Aminu Abdulsalam, tsohon dan takarar mataimakin gwamna daga tsagin Kwankwasiyya a Jihar Kano, cewa ya yi, “Wannan gyara da aka samu zai kara taimakawa wajen karfafa dimokuradiyya da karfafa gaskiya da dokokin zabe da kuma rage amfani da kudi don sayen masu kada kuri’a.
“Wannan doka ta haramta kuma ta kayyade kudaden da za a iya kashewa a kan harkar zabe, duk wanda ya yi wannan ya keta doka kuma doka za ta hau shi.”
4. Masu mukaman siyasa ba su so ba
Tsohon dan takarar gwamnan Jihar Kaduna, A cewar Sanata Shehu Sani, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Masu rike da mukaman siyasa ba za su so su ajiye mukamansu ba kafin tsayawa takara, shi ya sa ba su so aka sanya hannu kan dokar ba.”
Sai dai kuma a ranar Talata dai Shugaba Buhari ya aike wa Majalisa bukatar cire sashen da ya hana masu rike da mukaman siyasa kamar ministoci da sauransu tsayawa takara ko shiga zaben tsayar da ’yan takara, sai idan sun ajiye mukamansu.
Sabuwar bukatar ta Buhari dai ta sa masu sharhi na ganin har yanzu da sauran rina a kaba.
5. Sabon tsari a siyasa
“Dole a jinjina wa Shugaba Buhari kan sanya hannu kan sabuwar dokar zaben, saboda hakan zai samar da sabon tsari a siyasar Najeriya,” cewar Kwamared Akpabs.
6. Inganta tsarin zaben fid-da gwani
A bangaren Shugaban Kwamitin yada labaran majalisar dokoki, Sanata Ajibola Basiru, cewa ya yi sabuwar dokar za ta inganta yadda ake gudanar da zabe.
“Yadda ake gudanar da zabukan fidda gwani, kudaden yakin neman zabe, amfani da na’urorin zamani wajen gudanar da zabuka da kuma fitar da sakamakon ta intanet, sauye-sauye ne da za su tabbatar da sahihancin zabe.”
7. Buhari ya cancanci yabo
Sanata Aliyu Wamako, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, ya bayyana cewa Buhari ya nuna cewa dimokuradiyya na raye a Najeriya, kuma sanya hannunsa a kan dokar zai inganta tsarin yadda abubuwa da dama ke tafiya a harkar gudanar da zabuka.
8. Maye gurbin dan takarar da ya rasu
Mai magana da yawun majalisar dokokin Najeriya, Benjamin Kalu, ya ce, “Sadara ta 34 ta bai wa jam’iyyun siyasa damar gudanar da zaben fidda gwani don maye gurbin dan takarar da ya rasu a lokacin zabe.
“Tabbas wannan ci gaba ne kuma dole a jinjina wa majalisun kasar nan kan tsayawa kai da fata don cimma wannan hadafi.”
9. Kebe wa nakasassu gurbi
Abba Ibrahim ya ce, “Idan aka lura, za a ga cewa dokar da Buhari ya sanya wa hannu ta samar da gurbi na musamman ga masu bukata ta musamman, wanda a baya ba haka abun ya ke ba…”
10. Samun kudaden gudanar da zabe a kan lokaci
Shi kuma Abba Khalifa shaida wa Aminiya ya yi cewa, “Gyaran dokar zaben ya bai wa hukumar zabe damar samun kudaden da za ta gudanar da zabe shekara daya kafin zaben, a baya ba haka abun yake ba.
“INEC na shan wahala inda za ta rika fadi-tashi kan ganin gwamnati ta fitar mata da kudin da za ta yi amfani da shi wajen gudanar da zabe, wanda a wasu lokuta ya kan kai ga dage lokacin gudanar da zabe,” inji shi.