✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2022: Netherlands ta casa Amurka 3-1

Netherlands ta tsallaka zuwa Kwata-Fainal bayan lallasa Amurka da 3-1 a wasa mai daukar hankali ranar Asabar

Netherlands ta tsallaka zuwa matakin Kwata-Fainal bayan ta lallasa Amurka da 3-1 a Gasar Cin Kofin Duniya da ke gudana a kasar Qatar. 

Amurka ta kwashi kashinta a hannu a karawarta da kasar Netherlands ne a wani wasa mai daukar hankali ranar Asabar.

Nasarar tawagar ’yan wasan na Netherlands a wasan na zagaye na biyu ta tsallakar da su zuwa matakin Kwata-Fainal

A ranar Asabar aka fara arangama a zagayen ’Yan 16, bayan a ranar Juma’a an kammala Matakin Rukuni.

Tuni dai aka tisa keyar kasashe 16 zuwa gida a karshen Matakin Rukuni a Gasar Kofin Duniya ta farko a Yankin Gabas ta Tsakiya.

Kasashen da suka zo na daya da na biyu a kowane rukuni ne suka tsallaka zuwa mataki mataki na biyu — ’Yan 16.

A zagaye na biyun, sauran wasannin da za a fafata a ranar Asabar su ne tsakanin Argentina da Australiya; Faransa da Poland; Birtaniya da Senegal; Japan da Croatia; Brazil da Koriya Ta Kudu; Moroko da Spain; sai kuma Portugal da Switzerland.