✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qatar 2022: Mun sayar da tikitin kallon kwallo guda 3m —FIFA

Wannan shi ne adadi mafi yawa da FIFA ta taba samu a tarihin gasar

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta ce ta sayar da tikitin kallo kusan guda miliyan uku a Gasar Cin Kofin Duniya da yanzu haka ake yi Qatar.

Hakan, a cewar hukumar ya sa kudin shigarta ya karu zuwa Dala miliyan 7.5, kari ma fi girman da ta taba samu a tarihin kafuwarta.

Soma gasar ya haifar da karuwar mutanen da ke sha’awar zuwa kallon wasanni 64 da za a buga a tsawon kwana 29, duk da sukar da kasar Qatar ke sha tun da ta samu damar daukar nauyin gasar.

Jerin gwanon masu son shiga kallon wasannin sai karuwa yake yi a birnin Doha, inda ’yan kallo sukan shafe tsawon lokaci domin shiga shafin gasar domin sayen tikitin ta intanet.

Tuni yawan tikitin da aka sayar na shiga kallon wasannin ya zarce na gasar da aka yi a Rasha a 2018, wanda aka sayar da tikiti guda miliyan 2.4

Kakakin FIFA ya ce, ’yan kasashen Amurka da Saudiyya da Mexico da Birtaniya da Faransa da Haddiyar Daular Larabawa da Ajentina da kuma Brazil, su ne kan gaba a wajen sayen tikitin.

Jami’in na FIFA ya fada a wani babban taro cewa, hukumar na sa ran kudin shigarta zai iya kaiwa Dala bililyan 7.5 kafin karshen shekarar nan.