Kocin tawagar ’yan wasan Belgium, Roberto Martinez, ya ajiye aikinsa bayan kasar ta gaza zuwa zagayen ’yan 16 a Gasar Kofin Duniya ta 2022.
Belgium na da manyan ’yan wasa irin su Hazard, De Bruyne, Lukaku, Batsuyi, Carrasco da sauransu, amma sun gaza tabuka abin arziki a gasar da ke gudana a kasar Qatar.
- Mahara sun kashe mutum 7, sun sace 5 a sabon hari a Sakkwato
- Mutum Miliyan 25 Ke Dauke Da Cutar AIDS A Afirka —WHO
Belgium dai ta gaza fitowa daga rukuni bayan wasanni uku da ta kara da kasashen Kanada da Maroko da kuma Croatia, amma maki hudu ta samu, bayan cin wasa daya, rashin nasara daya da kuma kunnen doki daya.
Yanzu haka Maroko da Croatia ne suka tsallaka zuwa zagayen ’yan 16 na Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022.
Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa Roberto Martinez ya dade da yanke shawarar ajiye aikinsa tun kafin fara gasar a kasar Qatar.