Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya tagawar ’yan wasan Maroko da Sarkin kasar, Mohammed na Hudu murnar kafa tarihi a Gasar Kofin Duniya na 2022 da ake yi a kasar Qatar.
A sakon taya murna da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Litinin, Buhari ya yaba wa tawagar ’yan wasan bisa yadda suka yi bajintar zuwa matakin kusa da na karshe.
- Yadda ‘Cousin’ ke kawo tarnaki ga masoya
- NAJERIYA A YAU: ’Yan Bindiga Sun Zafafa Hare-Hare Bayan Samuwar Mai A Bauchi
Maroko ta zama kasa ta farko a Afirka da ta samu gurbin wasan kusa da na karshe a Gasar Kofin Duniya, tun bayan fara gasar 92 da suka gabata.
A sakon Buhari, ya ce, Maroko ta nuna bajinta da kuma ta goya Afirka da kwazonta, sannan kafatanin kasashen nahiyar na goyon bayanta ta lashe gasar.
Buhari ya yaba wa ’yan wasan bisa nuna kwarewarsu, wanda ya ce ba lallai su samu wannan gagarumar nasarar ba tare da gudunmawar hukumomin kasarsu ba.
Maroko ta kafa tarihin zuwa matakin kusa da na karshe bayan doke Sifaniya da Portugal tun bayan fitowa daga matakin rukuni na gasar.
Kazalika, ta kafa tarihi, inda babu wata kasa da ta jefa mata kwallo a raga tun da aka fara gasar.