An gudanar da taron jana’izar Shugaban Tarayyar Soviet na karshe, Mikhail Gorbachev, a Rasha, ba tare shugaban kasar, Vladimir Putin, ya halarta ba.
An yi taron ne ba tare da wani biki ba, a birnin Mosco a ranar Asabar, inda dubban mutane suka yi dogon layi domin yin bankwanan karshe ga Mista Gorbachev, wanda sojoji suka rako akwatin gawarsa.
- Yadda iyaye suka yi wa ’ya’yan cikinsu 48 fyade a shekara a 2
- An kama fasto ya yi wa ’yar shekara 12 fyade a coci
An gudanar da taron ne a babban dakin taro na Hall of Columns, wanda a cikinsa ake gudanar da tsaron jana’izar manyan jami’an gwamnatin kasar Rasha.
A nan ne aka fara ajiye gawar tsohon shugaban tsohon Shugaban Tarayyar Soviet, Joseph Stalin a tsawon kwana hudu na zaman makoki a fadin kasar a shekara 1953.
Duk da cewa a halin yanzu Rasha na fusktantar tsangwama daga kasashen duniya kan mamayarta a Ukraine, yawancin mahalarta taron jana’izar sun bayyana taron jana’izar Gorbachev a matsayin abin da ya bude kofar kasar ga sauran sassan duniya.
Mahalarta taron jana’izar dai sun hada da yara da matasa da dattawa da ke iya tuna yadda rayuwa ta kasance a zamanin Tarayyar Soviet, matasan kuma yawancinsu zamanin Putin kawai suka sani.
A ranar Talata Gorbachev ya rasu yana da shekaru “bayan fama da jinya”, a wani asibiti.
Ya jagoranci kasar daga 1985 zuwa 1991, kuma shi ne ya kawo sauye-sauyen da suka sama wa tsarin dimokuradiyya gindin zama a kasar, da kuma narkewar Tarayyar Soviet daga karshe.
Yana daga cikin mnayan shugabannin siyasa na karni na 20, kuma kasashen Yammacin duniya sun rika ganin sa a matsayin wani zaki bisa rawar da ya taka wajen kawo karshen yakin cacar baka da kuma kawo sauye-sauye a Tarayyar Soviet.
Duk da haka wasu al’ummar Rasha na ganin bakinsa saboda matsalar tattalin arzikin da kasar da kuma raguwar karfin ikonta da idon duniya sakamakon rushewar tarayyar.