Shugaban Rasha, Vladmir Putin, ya halarci gagarumin atisayen dakarun hadin gwiwa da sojin China a ranar Talatar nan.
Mai magana da yawun Fadar Kremlin, Dmitry Peskov ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
- Kwadayin kudi ke kai wasu ’yan kwallon Firimiyar Ingila —Kroos
- Nan da Disamba za mu murkushe ayyukan ta’addanci —Gwamnati
A ranar 1 ga watan Satumba ne aka fara atisayen sojin da aka yi wa lakabi da Vostok-2022 a can Gabashin Rasha, wanda ake sa ran kawo karshensa a ranar Laraba.
Gagarumin atisayen na hadin gwiwa da ya kunshi sojojin Sin da wasu kasashe masu kawance da Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da kashen duniya suka juya wa Rashar baya saboda mamayar da take yi a Ukraine.
Wannan ya kara tabbatar da kusancin da ke tsakanin Rasha da China da ke takon saka da manyan kasashen Yammacin Duniya.
Atisayen wanda aka faro a makon da ya gabata, rabon da kasar ta gudanar da irinsa tun a shekarar 2018.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce atisayen ya mayar da hankali wajen horar da sojoji yadda za su rika tare hare-hare ta sama da kuma dabarun kai samame ta sama a yankunan da suke shirin farmaka.
Wasu hotuna da ma’aikatar tsaron ta Rasha ta fitar sun nuna yadda jiragen yaki ke sauka da tashi cikin yanayi na salon kai farmaki.
Sojojin Rasha fiye da dubu 50 ke cikin atisayen tare da wasu manyan makaman yaki akalla dubu 5 ciki har da jiragen yaki 140 da kuma jiragen ruwa na yaki 60.
Wasu bayanai sun ce baya ga dakarun China da ke cikin atisayen na Rasha har da sojojin makwabtan kasar irin su Belarus da Siriya da Indiya.