Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin da takwaransa na China, Xi Jinping sun kaurace wa taron G-20 da yanzu haka yake gudana a India.
A yau Asabar aka buɗe taron manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi na G20, wanda a bana kasar Indiya ke karɓar baƙunci, sai dai biyu daga cikin ƙasashen da ke sahun gaba wato Rasha da China ba su halarci taron ba.
Tuni dai shugabannin ƙasashen suka taru a sabon ɗakin taron da aka gina a birnin Delhi.
Shugabannin na tattaunawa kan batutuwa masu muhimmanci ciki har da matsalar sauyin yanayi, da matsalolin da ƙasashe masu tasowa ke fuskanta, sai dai ana sa ran yaƙin da Rasha ta ƙaddamar a Ukraine ya mamaye taron.
Da alama akwai kyakkyawan fata, ganin yawancin shugabannin kasashen sun amince da buƙatar Firai Ministan Narendra Modina ta gayyatar ƙungiyar Tarayyar Afirka domin shiga cikinsu su tashi daga G20 zuwa G21.
Sai dai Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce abubuwa sun yi masa yawa, amma ana ganin kawai yana son kaucewa taron ne saboda gudun kada Kotun Duniya ICC ta kama shi, wadda a farkon shekarar ne ta ba da umarnin kama Putin kan zarginsa da aikata laifukan yaƙi a Ukraine.
Bayanai sun ce ana ganin za a tattauna matsalar wannan yaƙi a yayin taron na G-20.
Rasha ta bayyana abin da ake yi a Ukraine wani aikin soji na musamman maimakon mamayar ko kuma yaƙi.
Kazalika, Xi Jinping na zuwa kowanne taron G20 tun da ya fara shugabanci a China, sai wannan karon ne ya gaza halartar wannan, abin da shugaban Amurka Joe Biden ya ce ka iya zama cin fuska ga India.
Shugaba Xi da ya kaurace wa taron ya diga ayar tambaya kan muhimmancin kungiyar kasashen na G-20, kodayake ya aika firaministansa, Li Qiang domin wakiltar sa.
Babu dai wani gamsasshen uzuri da za a amince da shi a hukumance na rashin halartar shugaba Xi na China.
China dai babbar ƙawa ce ga Rasha kuma har yau ba ta ce uffan ba game da mamayar da ta yi a Ukraine.
Manyan takunkuman da ƙasashen yamma suka sanya wa Rasha ya ƙara ƙarfin cinikayyar da ke tsakaninta da China da kashi 30.