Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain na shirin sayar da ’yan wasanta akalla 10 a kokarin ta na neman kudi saboda shirin kulla yarjejeniya da tsohon dan wasan Barcelona, Lionel Messi.
Kafofin wasta labaran wasanni sun bayyana cewa hakan ne kadai zai sa kungiyar ta kaucewa karya dokar haramta kashe kudaden da suka zarce wadanda take samu, dokar da ake kira Financial Fair Play a turance.
Jaridar wasanni ta Team Talk ta ruwaito cewar, bayan samun tabbacin Messi zai bar Barcelona, kungiyar mai buga gasar Ligue 1 ta gaggauta daukar matakin shirya sai da ’yan wasan nata da dama kafin kulla yarjejeniya da Messi nan da ’yan kwanaki.
Daga cikin ’yan wasan da PSG ta sanya a kasuwa akwai, Idrissa Gueye, Rafinha, Mauro Icardi, Abdou Diallo, Thilo Kehrer da kuma Ander Herrera.
A halin yanzu kungiyar tana da manyan masu tsaro raga akalla takwas, inda biyar daga ciki suka kasance zabinta na farko.
Daga cikin manyan gololin da PSG take da su akwai Keylor Navas, Gianluigu Donnarumma, Sergio Rico, Denis Franchi da Alexander Letellier.
Sai dai a halin yanzu akwai rashin tabbas game da makomar Kylian Mbappe a PSG idan yrajejeniyar sa da ita ta kare a shekara mai zuwa.
Kungiyar na fatan zuwan Messi zai shawo kan dan wasan na Faransa ya ci gaba da zama tare da ita.
Tun a makon jiya ne PSG ta soma tattaunawa da wakilan dan wasan mai shekara 34 bayan ya gaza kulla sabuwar yarjejeniyar da Barcelona.
Bayanai sun ce bangarorin biyu sun yi tattaunawar farko a ranar Alhamis kuma a ranar Asabar suka ci gaba da ganawa domin amincewa da kwangilar da za ta kai ga Messi ya koma Faransa a kwangilar shekara biyu.