Paris Saint-Germain ta tabbatar da sayen Golan AC Milan, Gianluigi Donnarumma, kwanaki bayan ya taimaka wa Italiya ta lashe gasar Euro 2020.
A watan Yuni ne Donnarumma ya bar AC Milan, bayan kwantaraginsa ya kare da kungiyar mai buga gasar Serie A.
- Hayaniya ta kaure a Majalisar Wakilai kan dokar man fetur
- Mathew Kukah ya sake caccakar gwamnatin Buhari
Dan wasan mai shekara 22, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da za ta dauke shi zama a PSG har zuwa watan Yunin shekarar 2026.
Tun a Larabar da ta gabata ce Donnarumma ya rubuta wata budaddiyar wasiki zuwa ga magoya bayan AC Milan, kwana guda gabanin komarwasa PSG.
A lokacin da yake shekara 16 kacal, Donnarumma ya samu shiga babbar tawagar AC Milan bayan an dauko shi daga tawagar Matasa ta kungiyar a shekarar 2015.
Tun daga wannan lokaci likafarsa ta daga, inda ya zama mai tsaron raga zabin farko, kuma ya ci gaba da zama a matsayin har zuwa lokacin da ya bayar kungiyar a bana.