Alhaji Falalu Bello shi ne shugaban Jam’iyyar PRP na kasa, inda a wata hira da ya yi a shekarar 2020, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta yi bakin kokarinta wajen doke jam’iyyun APC da PDP a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
A hirar da ya yi kwanan nan da jaridar Daily Trust ya ce an sake fasalin jam’iyyar kuma a shirye take ta samar da shugaban kasar Najeriya.
Jam’iyyar PRP ba ta gabatar da dan takarar Shugaban Kasa a zaben da ya gabata amma a kwanakin baya ka ce yanzu an sasanta, me ya canza?
Idan za a iya tunawa, Jam’iyyar PRP jam’iyyar siyasa ce tun a 1978, duk jam’iyyun da suka zo da PRP irin su UPN, NPN, GNPP duk sun tafi.
Don haka, ita tsohuwar jam’iyya ce da ta dade tana gwagwarmaya a kasar nan na tsawon lokaci. A gaskiya, ba a samu wani ci gaba sosai ba a cikin jam’iyyar.
Amma a yanzu a matsayinmu na shugabannin jam’iyyar cikin shekara uku nan, tun da muka karbi jagorancin Jam’iyyar PRP, muke ta kokarin ganin mun shiga zabe, domin mu yi rajistar cewa jam’iyyar ta dawo.
Misali a zaben 2019, mun fitar da ’yan takara 385 a jihohi 22 cikin jihohi 36 na kasar nan, hakan na nuni da cewa hakika mun dawo muna nan daram.
Abin da muke kokarin yi shi ne idan kana da dan takara da zai yi yakin neman zabe, zai zagaya kuma ya daga tutarmu hade da sanya hotunansa da tambarin jam’iyyarmu, yin hakan zai nuna wa jama’a cewa Jam’iyyar PRP ta nan.
Ba mu dade da gama taron jam’iyyar a matakan jihohi ba, mun gudanar a jihohi 30 daga cikin jihohi 36 da muke da su.
Mun zabi mambobin Kwamitin Gudanarwa a jihohi shida ciki har da ta bakwai, wato Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Don haka a yau a Najeriya muna nan a kananan hukumomi 733 ko ta hanyar yin taro ko kuma ta hanyar yin nadi.
To a aikace dai, abin da wannan ke nufi shi ne jam’iyyar ta dawo da ranta.
Shin kuna ganin a matsayinku na jam’iyya za ku iya yin tasirin da ake so har ku ci zabe ko kuma kun dogara ne kan batun hadewar da ake shirin yi?
Ba mu damu da shiga cikin hadaka ba ko kawance da wata jam’iyya, kuma muna cikin tattaunawa.
Dubi yadda PDP da APC suka mayar da zaben kasar nan harkar kudi, suka mayar da komai sai kudi kawai, don fuskantarsu akwai bukatar yin hadaka da kawance kuma za mu yi haka.
Amma a gaskiya, idan har za mu iya samun abin da muke da shi na yawan mambobinmu a Kebbi da kuma duk jihohin kasar nan, za mu iya tafiya mu kadai kuma mu ci nasara.
Ba abu ne mai yiwuwa ba. Idan har aka ce muna da mambobi 30,000 a duk jihohi 36 hada da Birnin Tarayya Abuja za mu iya samun nasara cikin kwanciyar hankali.
To, shin a yanzu wanne kuke ciki, hadewar ko kuna so ku tafi ku kadai?
Bari mu dauki misali, PRP tana kawance da Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC); mun yi imani da abin da suka yi imani da shi, amma idan za mu iya shiga cikin wata irin dangantaka da NLC da TUC za su kira dukkan mambobinsu su ce ku zabi PRP, shin hakan ba zai taimake mu ba?
Don haka bai kamata mu kauce wa yin kawance ko hadewa ba. Kuma muna tattaunawa da su.
A gaskiya ma, dai a wani lokaci na jagoranci kwamitin hadaka na NCFront don haka muna tare kuma ba mu za mu yi watsi da hakan ba.
Mece ce matsayar jam’iyyarku a kan shiyya-shiyya?
Shiyya-shiyya ba ya cikin tsari, tsarin Jam’iyyar PDP ce; zan iya ba ku kwafin tsarin mulkinmu.
Babu inda muka ce za mu yi shiyya ga ofisoshinmu. Tabbas kundin tsarin mulki ya ce a raba ofisoshi, misali, KwamitinZartarwa na Kasa, za mu iya karkasa shi ga ko’ina.
Mu ce Shugaban Kasa ya fito daga Kogi, Mataimakin Shugaban Kasa ya fito daga Neja? A’a, ba na jin za mu yi hakan. Ba na tsammanin za mu yi haka, za mu bar komai a bude.
Wani abin mamaki me ya sa a kwanan baya wani bangare ya bulla a cikin jam’iyyar. Wadanne batutuwa ne ake jayayya a kai?
Wannan shi ne abin da Najeriya ke ciki, in ba haka ba, me ya sa suke yin haka?
A matsayina na Shugaban Jam’iyyar PRP a yau babu wanda ya rubuto mani daga bangarensu ya ce wannan shi ne abin da na yi kuskure ko na rubuta mana kan wani lamari a matsayina na shugaba.
Me ya sa suke adawa da shugabancinku?
Duk wanda yake da takardar shaidar dan jam’iyya, kuma hukumar zabe ta kasa ta amince da shi, shi ne zai fitar da ’yan takarar zabe, amma za su iya ci gaba da hayaniya. Ina da asalin shaidar rajista kuma INEC ta amince da mu a matsayin shugabannin jam’iyyar na gaskiya.
Kuna cewa rikicin alama ce ta ci gaba a jam’iyyar?
Abin dai abin takaici ne. Shekara uku baya wane ne yake jin labarin Jam’iyyar PRP sai a ’yan shekarun nan hudu da suka wuce. Don haka, a zahiri babu wanda ya damu da jam’iyyar.
Amma yanzu mutane sun damu saboda muna samun nasara ta kowace hanya. Da mun kasa da ba za su nuna damuwarsu ba