✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PRP za ta binciki dan takararta na zaben Gwamnan Osun

PRP ta janye jajibirin zaben Gwamnan Jihar Osun, ta kafa kwamitin ladabtar da dan takararta

Jam’iyyar PRP ta kafa kwamitin ladabtar da dan takararta na Gwamnan Jihar Osun, ta kuma janye daga zaben kimanin awa 24 kafin a fara gudanar da shi.

Jam’iyyar ta ce za ta gudanar da bincike kan dan takararta na gwamna, Ayowole Adedeji, sannan ta bukaci mambobinta da su karkatar da hankalinsu kan zaben 2023 da ke tafe.

Sakataren PRP na Kasa, Kwamred Babatunde Alli, ya sanar  a ranar Alhamis cewa, “Jam’iyyar na takaicin rashin katabus din dan takararta na gwamna, Ayowole Adedeji da kuma tasirin hakan ga jam’iyyar a matakin Jihar Osun da ma kasa baki daya.

“Mun yi nazarin duk abubuwa da suka kamata, kuma mun yanke shawarar janyewa daga zaben gwamnan Jihar Osun na ranar 16 ga watan Yuli, 2022.

“Uwar jam’iyya na umartar reshen Jihar Osun ya kafa kwamitin ladabtarwa mai mutum biyar domin bincikar dan takarar.

“Kwamitin zai binciki dalilinsa na ci gaba da zama a kasar waje tun bayan da ya zama dan takara, ya ki dawowa sai saura mako biyu a yi zabe, wanda hakan ya hana jam’iyyar gudanar da yakin neman zabe yadda ya kamata.

“Jam’iyya na kira da maboninta a Jihar Osun da su karkatar da hankalinsu zuwa yadda za ta kai ga nasara a babban zaben 2023 da ke tafe.”