✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pobga ya sanya takalmansa a kasuwa don ya tallafa wa gajiyayyu

Rahotannin da ke fitowa daga Faransa sun ce shahararren dan kwallon Manchester United din nan Paul Pogba zai yi gwanjon takalman kwallonsa da ya lashe…

Rahotannin da ke fitowa daga Faransa sun ce shahararren dan kwallon Manchester United din nan Paul Pogba zai yi gwanjon takalman kwallonsa da ya lashe Kofin Duniya da su don ganin ya yi amfani da kudin don tallafa wa wata makaranta da ke daukar nauyin ’ya’yan talakawa.

An kiyasta takalman za su kai Dala dubu 56 da 500 (kimanin Naira miliyan 20 da dubu 216).

Pogba ne ya zura kwallo ta uku a ci 4-2 da suka doke Kuroshiya a wasan karshe na cin Kofin Duniya da aka yi a Rasha a bara, kuma takalman kwallo ne yake son ya yi gwanjonsu da ya mika kudin ga wata cibiya da take tallafa wa gajiyayyu da ke Faransa don kula da ’ya’yan marasa galihu da ke yin karatu a wata makaranta.

Pobga wanda ya taso a wani yankin da talakawa ke zaune a Faransa ya bayyana alhinin ganin yadda ’ya’yan marasa galihu suke fuskantar matsalar rayuwa a Faransa da hakan ta sa ya yanke shawarar sayar da takalman don ya tallafa wa marasa galihu.

Rahoton ya ce baya ga takalman, Paul Pogba zai sanya rigar kwallon da ya yi amfani da ita a wasan da Faransa ta yi da Iceland a gasar cin Kofin Nahiyar Turai a 2016 inda Iceland ta doke Faransa a wasan kusa da na karshe, kuma Fotugal ce ta  lashe kofin a shekarar.

“Na yi imanin wannan cibiya za ta tallafa wa gajiyayyu kamar yadda ni ma na ci irin wannan gajiya a lokacin da nake karami,” inji Pogba.

Ana sa ran za a yi gwanjon kayayyakin dan kwallon ne a ranar 29 ga wannan wata a Paris Babban Birnin Kasar Faransa.