Ana zargin karnuka sun kashe wani jami’in tsaron gidaje a yankin Lekki a Jihar Legas, bayan da karnukan suka tsere daga gidan mai su.
Wani bidiyo da @itzbasito ya wallafa a X, an ga karnukan suna yawo a kusa da gawar mutumin da ke kwance a kasa.
Ya wallafa a jikin bidiyon cewa, “Jiya da dare a Pinnock Estate wani mai gida bai kulle karnukansa yadda ya kamata ba, inda suka tsere suka kashe wani mai tsaron Estate ɗin har lahira,” in ji shi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce, “An kama mai karnukan kuma yana hannunmu.”
Masu amfani da kafofin sada zumunta sun bayyana damuwa kan kashe jami’in tsaron yayin da wasu ke neman a yi adalci, wasu kuma suke zargin cewa an yi rufa-rufa ne.
A cewar Redrum-MUFC, “Karnuka ba su yi haka, wannan dai akwai rufa-rufa. Galibi idan karnuka suka yi kisa irin wannan, ba sa barin gawar sai sun yaga jikinta.
“Jama’a muna ganin jini a kasa, amma babu tabon jini a jikin karnukan,” in ji shi.
Amma Oluwamooregrin ya nuna shakku kan alamar shigar karnuka a cikin ayyukan.
“Ba na jin boerboels za su iya yin haka sai idan an horar da su da cin danyen nama, labarin bai cika ba kuma yaya girman rukunin gidajen yake, har ba a lura da gudu da ihun mamacin ba?,” in ji shi.
Sai dai Clover Lavender ya jaddada cewa ya kamata mai karnukan ya fuskanci fushin doka.
“Dole ne a daure mai karnukan kuma a kulle shi har abada,” in ji shi.