Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu.
Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya zama shugaban rundunar a ranar 19 ga watan Yuni, 2023, ya rasu ne a ranar Talata bayan rashin lafiya.
Allah Ya yi masa rasuwa yana da shekaru 56, ya bar matarsa Mariya, da ’ya’ya biyu.
Fadar Shugaban Kasa ta sanar da rasuwar ta hannun Hadimin Shugaban Kasa Kan Yada Labarai, Bayo Onanuga, yana mai mika ta’aziyyar Shugaba Bola Tinubu game da babban rashin.