✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Platini ya sake zama shugaban Hukumar UEFA

A ranar Talata da ta wuce ne aka sake zabar Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) Michel Platini a karo na uku a…

A ranar Talata da ta wuce ne aka sake zabar Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai (UEFA) Michel Platini a karo na uku a jere.

Platini dan kimanin shekara 59 an fara zabarsa a wannan matsayi ne tun cikin shekarar 2007.
daukacin kasashe 54 da suka kada kuri’a ne suka zabi shugaban ba tare da ya samu hamayya ba.
Shugaban ya bayyana farin cikinsa a kan wannan zabe da aka yi masa, kuma ya sha alwashin cigaba da kawo sababbin tsare-tsare a Hukumar don ganin ya cigaba da bunkasa harkar kwallo a Nahiyar Turai da ma a duniya baki daya.
Da wannan zabe da aka yi masa, zai cigaba da rike mukamin Mataimakin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) mai wakiltar Nahiyar Turai.
A duk bayan shekaru hudu ne ake sake zabe a Hukumar UEFA, don haka Platini zai cigaba da jan ragamarsa har zuwa shekarar 2019.