A yau Alhamis an sanar da Amaju Pinnick a matsayin wanda aka sake zaba shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF).
Pinnick ya doke abokan hamayyarsa uku wadanda suka hada da: tsohon shugaban hukumar Aminu Maigari da Taiwo Ogunjobi da kuma Chinedu Okoye da kuri’u 34 don ci gaba da zama shugaban hukumar NFF.
An bayyana sakamakon zaben kamar haka Maigari ya samu kuri’u takwas yayin da Ogunjobi ya samu biyu, yayin da Okoye bai samu ko kuri’a daya ba.
Zababben shugaban Pinnick ya samu kuri’u 34 daga 44 da aka kada a zaben.
Shugaban kwamitin zaben hukumar NFF Muhammad Kotu ne ya bayyana sakamakon zaben.