✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pillars Para Soccer ta lashe kofin kwallon guragu na kasa

kungiyar kwallon Guragu ta Jihar Kano mai suna Kano Pillars Para Soccer ce ta zama zakara a gasar wasan kwallon guragu na kasa da aka…

kungiyar kwallon Guragu ta Jihar Kano mai suna Kano Pillars Para Soccer ce ta zama zakara a gasar wasan kwallon guragu na kasa da aka kamala a rufaffan dakin wasa na Sani Abacha da ke kofar Mata a birnin Kano.
kungiyar ta Jihar Kano ta zama zakara ne a gasar bayan ta doke Jihar Katsina da ci biyu da nema a wasan karshe da suka buga a karshen makon da ya gabata yayin da Jihar Nassarawa ta zama ta uku.
Da yake rufe gasar tare da mika wani katafaren kofi ga kungiyar kwallon guragu ta Jihar Kano da ta zama zakara, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Alhaji Kabiru Alasan Rurum ya tabbatar da cewar gwamnatin Kano za ta ci gaba daukar matakan da suka kamata domin bunkasa harkokin wasanni na masu bukata ta musamman.
Shugaban Majalisar wanda Shugaban Kwamitin Wasanni na Majalisar Alhaji Ayuba Labaran ya wakilta ya bayyana kwallon guragun a matsayin wata hanya da ke samar da ayyukan yi ga guragun a maimakon  yawon barace-barace a tituna.
A nasa jawabin Shugaban Hukumar Wasanni na Jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima ya bayyana gasar da cewa ta ba hukumarsa damar ci gaba da shiri akan yadda kungiyar kwallon guragu ta Jihatr Knao za ta yi wa  jihar Kano kyakkyawan wakilci a gasar wasanni guje-guje da tsalale-tsalle ta kasa da za a gudanar a watan Nuwambsr wanann shekara a garin  Kalaba ta Jihar Kross Riba.
Alhaji Galadima ya ja hanakalin dukkanin ’yan wasan da suka halarci gasar da su dauka cewar kowannensu ya yi nasara bisa la’akari da yadda suka kwashe makonni biyu suna barje gumi kuma  aka kamala ba tare da samun matsala ba.
Da ayke jawabi Shugaban da ke kula da wasan kwallon guragu ta kasa, Alhaji Musbahu Lawan Didi godewa gwamnati da al’ummar Jihar Kano ya yi saboda hadin kai da gudummowar da suka bayar inda aka gudanar da wasan cikin nasara.
A wani ci gaban kuma a ranar Litinin din da ta gabata aka gudanar da wani wasan kwallon kafa tsakanin kungiyar kwalllon Kurame ta Jihar Kano da takwararta ta Jihar Jigawa.
Wasan wanda aka gudanar a dakin wasa na Sani Abacha da ke Kano ya ba wakilan Jihar Kano damar samun nasara da ci daya mai ban haushi.
Da yake jawabi a wajen wasan Mataimakin Gwamnan Kano akan harkokin Masu Bukata ta Musamamn Alhaji Ali Adnan  Daneji ya bayyana cewa an shirya wasan ne don kara karfafa zumuncin da ke tsakanin kuramen jihohin biyu, musamamn wadanda ke karatu a makarantun kula da nakasassu da ke ciki da wajen jihar.