✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Peter Obi ya ziyarci waɗanda harin masallaci ya rutsa da su a Kano

Taƙaddamar rabon gado ce ta janyo mutuwar mutanen a ƙauyen Larabar Albasawa da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a Jihar Kano.

Ɗan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a Zaɓen 2023, Peter Obi, ya ziyarci waɗanda harin masallaci ya rutsa da su a Jihar Kano.

Peter Obi wanda a wannan Lahadin ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano, kai tsaye ya wuce Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, inda wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa ke jinya.

A jawabinsa, Peter Obi ya ce, “wannan abu ne mai ban tsoro da dole a yi Alla wadai da shi.

“Abin baƙin ciki ne irin wannan lamari na iya faruwa a ƙasarmu a yau.

“Ba wanda zai iya faɗin wani dalili da zai sanya wannan matashi ya kai wa ’yan uwansa irin mummunan hari.

“Duk da haka ba za mu daina yin Allah wadai da irin wannan aika-aikar a kan mutane ba.

“Dalilin wannan ziyara da na kawo shi ne jajanta wa waɗanda lamarin ya shafa da nuna damuwa kan irin raɗaɗin da suke ɗanɗanawa.

“Kazalika, na kawo wannan ziyara ce domin bai wa mahukuntan wannan asibiti goyon baya da ƙara musu ƙarfin gwiwa kan kulawar da suke da waɗanda harin ya rutsa da su.

Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya kuma jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Kano, yana mai kira ga duk ’yan Nijeriya da su haɗa kai wajen yaƙar irin wannan lamari da ya bayyana a matsayin rashin hankali.

Aminiya ta ruwaito yadda taƙaddamar rabon gado ta janyo mutuwar fiye da mutum 10 a ƙauyen Larabar Albasawa da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a Jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce bincike ya nuna cewa, ana zargin wani mutum, Shafi’u Abubakar mai kimanin shekaru 38 ya jefa wata roba ne ɗauke da fetur cikin wani masallacin, sannan ya cinna wuta.

Bayanai sun ce matashin ya cinna wa masallatan wuta ne da misalin ƙarfe 5:30 suna tsaka da sallar Asubah.

Ana fargabar cewa matashin bayan cinna wutar ya rufe ƙofar masallaci da ya rutsa da aƙalla da mutum 40.

Kimanin mutum 14 dai tuni sun riga mu gidan gaskiya yayin da ragowar ke ci gaba da samun kulawa a asibiti.