✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An soma aikin ceto bayan Shugaban Iran ya yi hatsarin jirgin sama

Tuni aka tura masu aikin ceto wurin da ake zargin hatsarin ya faru domin gano wurin da aka yi hatsarin.

Wani jirgin sama mai saukar ungulu ɗauke da Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya yi hatsari a ranar Lahadi.

Sai dai gidan talabijin ɗin ƙasar da ya ba da tabbacin aukuwar lamarin bai yi ƙarin haske kan halin da shugaban yake ciki ba.

Daga cikin mutanen da ke cikin tawagar shugaban akwai Ministan Harkokin Waje, Hossein Amirabdollahian, da Gwamnan lardin gabashin Azerbaijan, Malik Rahmati, da limamin Juma’a na Tabriz, Muhammad Ali Al Hashem.

Kafar watsa labaran ƙasar ta ce lamarin ya faru ne a kusa da Jolfa, wanda birni ne da ke kan iyaka da Azerbaijan, kilomita 600 daga Tehran babban birnin ƙasar.

Masu aikin ceto sun yi ƙoƙarin zuwa wurin, amma rashin yanayi mai kyau ya kawo musu cikas sakamakon ruwan sama da iska mai ƙarfi.

Raisi ya je Azerbaijan da sanyin safiyar Lahadi domin ƙaddamar da wata madatsar ruwa tare da Shugaban Azerbaijan, Ilham Aliyev. Dam din dai shi ne na uku da kasashen biyu suka gina a kan Kogin Aras.

Iran na da jirage masu saukar ungulu da dama, sai dai irin takunkuman da aka saka wa ƙasar, ba ta iya samun kayayyakin gyaran jiragen cikin sauƙi.

Wasu daga cikin jiragen da ake amfani da su a ƙasar tun na zamanin juyin juya halin da aka yi a ƙasar a 1979.

Tuni aka tura masu aikin ceto wurin da ake zargin hatsarin ya faru domin gano wurin da aka yi hatsarin.

Shugaban Ma’aikatan Sojojin Iran, Manjo Janar Mohammad Bagheri ya bayar da umarni ga sojojin ƙasar da su yi amfani da duk wasu hanyoyin da suke da su wurin taimakawa don gano wurin da hatsarin ya faru.

Dan majalisar dokokin ƙasar mai wakiltar birnin Azerbaijan, Ahmad Alirezabeigi, ya shaida wa manema labarai a birnin Tehran cewa har yanzu masu aikin ceto ba su iya gano inda jirgin da ke ɗauke da shugaban ƙasar yake ba.

Tuni aka soma taruwa a wurare da dama na Iran ɗin inda ake yi wa shugaban ƙasar addu’o’i.