✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta shirya kwace mulki daga APC a 2023 — Saraki

Manyan ’yan APC za su sauya sheka su koma jam'iyyar PDP.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce jam’iyyar PDP ta shirya kwace mulki daga hannun APC a zaben 2023.

Saraki ya kuma ce wasu manyan ’yan siyasa a jam’iyyar APC mai mulki za su sauya sheka zuwa PDP kafin zaben, inda ya ce ba ya tunanin komawa APC.

A cewarsa, Najeriya na cikin mawuyacin hali kuma ’yan kasar sun ga abin da APC mulki ta yi musu.

Ya ce, “Mu ne kawai mafita ga ’yan Najeriya don samun kyakkyawan shugabanci.

“Dole ne kuma mu gamsar da ’yan Najeriya cewa a shirye muke mu karbi mulki.”

Ya bayyana haka ne a hirar da gidan talabijin na Arise a ranar Talata, inda ya ce zai ci gaba da zama a jam’iyyar PDP a 2023.

Ya ce, “Muna sa ran sauya sheka daga jam’iyya mai mulki; Idan kana bibiyar al’amurran siyasa, za ka ga manyan ’yan siyasa ba sa sauya sheka da wuri, sai a karshen lokaci, don haka a ci gaba da sauraro.”

Saraki na wadannan kalaman ne lokacin da yake amsa tambaya game da yiwuwar komawarsa jam’iyyar APC idan ya gaza samun tikitin takarar Shugaban Kasa a PDP.

“A kan tambayar cewa idan na yanke shawarar tsayawa takara ban samu tikitin ba, shin zan sauya sheka? Ina ganin hakan ba gaskiya ba ne.

“A 2015, na yi takarar Shugaban Kasa ban samu ba, amma na bayar da kaina na zama shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku, kuma na tsaya na yi aiki kai da fata.

“Abin da ke da muhimmanci ga duk wani dan PDP mai kaunar jam’iyyar kuma ya damu da kasa shi ne ya fara samun jam’iyya.

“Tun a bara wasu mutane sun riga sun yi magana game da burinsu na 2023, kuma na ce ba zai iya zama wani buri ba a yanzu, amma muna bukatar gina jam’iyya mai karfi.

“Don haka, abin da na fi mayar da hankali a  yanzu shi ne mu gina jam’iyya mai karfi, kuma mun fara gudanar da ayyuka a majalisarmu, da yin sulhu, gabanin babban taronmu.”